Daliban kasar Ghana 140 ne suka samu guraben karo karatu na jakadan kasar Sin dake kasar, saboda kwazon da suka nuna a fannin nazarin harshen Sinanci, a yayin wani biki da aka shirya a jami’ar Cape Coast (UCC).
Da yake jawabi a yayin bikin jiya Jumma’a, jakadan kasar Sin dake kasar Ghana Lu Kun, ya bayyana fatan samun tallafin karatun, zai taimakawa daliban Ghana a dukkan matakai wajen yin fice a fannin nazarin harshen Sinanci.
Jakada Lu Kun ya bayyana cewa, yayin da kasar Sin ta zama kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, koyon Sinanci zai taimaka ba wai kawai wajen karawa daliban fahimtar kasar Sin ba, har ma da raba ra’ayin ci gaban kasar ta Sin da kuma cimma burin da suke fata.
Lu ya ba wa daliban tabbacin cewa, a shirye ofishin jakadancin kasar Sin dake Ghana yake, wajen ba da taimako ga ‘yan Ghana masu son yin karatu a kasar Sin.
A nasa jawabin, mataimakin shugaban jam’iyyar UCC, Johnson Nyarko Boampong, ya ce muhimmancin koyon harshen Sinanci na dada karuwa. (Ibrahim Yaya)