Daliban Nijeriya shida, sun yi nasarar lashe gasar gwanayen koyo bayan rubuta jarrabawa a makarantar Sakandire ta Cambridge, wadda aka gudanar a watan Yunin shekarar 2023.
Darakta a ofishin hukumar kula da al’adun Birtaniya da ke Nijeriya, Lucy Pearson ce ta bayyana haka; ranar Alhamis a ofishin hukumar da ke Legas lokacin da aka bikin karramawa daliban.
- Jami’o’i 67 Sun Yaye Dalibai 6,464 Masu Digiri Mai Daraja Ta Daya Cikin Shekara 3
- Lokaci Ya Yi Da Nijeriya Za Rika Fitar Da Manja Kasashen Waje – Kungiyar Dalibai
Hukumar kula da al’adun Birtaniya tare da hadin gwiwar hukumar kula da jarrabawa ta Cambridge, su ne suka shirya wa wadannan dalibai wannan biki na karramawa; saboda irin kwazo ko hazakar da suka nuna wajen lashe gasar gwanayen koyo na makarantar ta Cambridge.
Pearson ta kara da cewa, wannan karramawa; ta kunshi daliban da suka fi samun maki mai yawa a jarabawar Turanci, a matsayin harshe na biyu.
Ta ci gaba da cewa, dalibai ‘yan Nijeriya biyu ne suka samu nasara a wannan jarrabawa ta watan Yunin shekara ta 2023, yayin da kuma wasu dalibai hudu; su ma suka taba samun irin wannan nasarar jarrabawar a watan Nuwambar 2023, dukkanin daliban shida sun fito ne daga makarantun Brookstone, James Hope College, Lagos da kuma ‘The Ambassadors Group of Schools’.
”Oluwademilade Dabid da Omaghomi Sharon daga makarantar Brookstone, su ne suka samu wannan nasarar cin jarrabawa da aka gudanar a watan Yunin 2023, yayin kum Obodoechi Chiedozie, Fabour Chinecherem da kuma Fehintoluwa Erinayo daga makarantar James Hope College da ke Jihar Legas, sai kuma Bamidele Sharon daga makarantar Ambassadors Group of Schools, su ma suka samu irin wannan nasara a watan Nuwambar 2023.
Daraktar ta kara da cewa, dalibai 95 daga makarantu 37 wadanda ke hulda da hukumar al’adu ta Birtaniya; baki-dayansu sun cancanci yabo, sakamakon samun maki mai yawa; wanda ya zarta na kowa a tsakanin makarantun da hukumar ke hulda da su a Nijeriya.
Har ila yau, “Darussan sun hada da na halayyar Dan’adam, fasahar sadarwa ta zamani da kuma harkar kasuwanci.
“Ana karrama dalibai ne, wadanda suka fi samun maki mai yawa a duk jarrabawar darasi daya ta duniya.
“Bugu da kari, dalibai 71 ne a Nijeriya; suka samu wannan babbar karramawa, sakamakon samun makin da suka yi a kasar da ake bai wa kowa nasa darasin ya rubuta tasa jarabawar.
“Karramawar ba ta tsaya a nan kadai ba, domin kuwa ta hada da dalibai 48 da aka karrama da kuma wasu guda takwas da suka samu karramawar da ta fit a kowa a darussa daban-daban.
Haka nan ta bayyana cewa, “sun yi amfani da tsarin da ya fi dacewa wajen zaben wadanda suka cancanta a karrama su, sakamakon irin kwazon da suka nuna a dukkanin darussan da suka koya. Sannan, abin bai tsaya a nan ba; domin kuwa har a kowane matakin ilimi, kamar yadda ta bayyana.
Da take yin karin haske dangane da tagomashin da za a iya samu sakamakon dalilin karramawar saboda samun maki mai yawa,, Pearson ta ce a fadin duniya irin nau’o’in jarabawar da aka amince da su suna taimaka wa dalibai samun zuwa jami’o’i masu nagarta da kuma samun aiki mafi tsoka.
Ta ce kuma su kasance masu samun rayuwa mafificiya, inda ta kara nuna farin cikinta na nuna cewar ai abin alfhari ne ga ita hukumar domin yin hulda tare da makarantun wajen yadda lamarin ilimi yake a Daular Turawa da kuma au’o’in ilimin da ake da shi a Nijeriya.
Shi ma darekatan shiyya na Afirka kudu da sahara na ilimin kasa da kasa a jami’ar Cambride, Mista Juan Bisser, ya taya wadanda suka samu nasara masu koyo daga Nijeriya, saboda irin kwazon da suka samu a Nijeriya wajen jarabawar watannin Yuni da Nuwamba 2023.
Bisser ya ce shi tsarin lamarin ilimi da ya shafi koyo da koyarwa an tsara shi tare da lura sosai domin ya taimaka wa masu koyo su samu hanyar bunkasa basirarsu.
“Lamarin karramawar da tafi kowace daraja an lura ne da irin kokari ko kwazon da aka yi wanda ba kowa bane yake samu burin hakan a jarabawar da ake yi a duniya da ta shafi jami’ar Cambridge.
“Karramawar ta yi nuni da irin kwazo da maida hankali na masu koyon sanin ilimi ga kuma uwa uba jajircewa ta malamai da iyaye.
“Da ilimin da daliban suka samu, masu koyo na Cambridge sun shirya sosai wajen samun damar wasu hanyoyi wadanda ke gabansu da za su taimaka masu wajen cimma burinsu,”.
Da yake jawabi a madadin wadanda aka karrama, Oluwademilade Dabid cewa ya yi lamarin ya burge su da aka ga har sun cancanta.Ya yi kira da daliban Nijeriya su maida hankali kan karatunsu.