Kungiyar Dalibai ta Nijeriya, ta yi kira ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi kokarin kyautatawa tare da farfado da harkokin sarrafa manja, wanda Allah ya wadata kasar da shi, ta yadda za a wadata ‘dan Nijeriya da shi, har ma da fitar da shi zuwa wasu kasashen ketare; kamar yadda aka saba yi a she-karun baya.
Kungiyar daliban, ta kalli muhimmancin hakan ne; sakamakon ganin yadda Allah ya wadata kasar da wannan arziki na manja, ta yadda idan aka rungumi shirin tare da kulawa das hi yadda ya kamata, ko shakka babu; harkokin tattalin arzikin kasar zai bunkasa, musamman ta fuskar sama matasa aikin yi da kuma mata.
- Matasa Za Su Amfana Da Shirin Noma Don Samun Riba
- Manoma Na Bukatar A Yi Rangwamen Kayan Aikin Noma – Wasu Jami’ai
Kiran kungiyar daliban (NANS), na zuwa ne bayan Shugaban Kungiyar Masu Samar da Manja ta Nijeriya, Mista Alphonsus Inyang ya bayyana cewa, Nijeriya a kowace shekara Nijeriya na batar da kimanin sama da daa miliyan 600, wajen shigo da Manja daga kasashen ketare; duk kuwa da cewa, Allah ya wadata ta da samun arzikin kwakwar Manja, mai dimbin ya-wan gaske.
Har ila yau, akwai kasashe da dama wadanda suka dogara da wannan Kwakwar Manja, a matsayin abin day a fi kawo wa kasashen nasu kudin shiga, amma Nijeriya na yin wasa da wan-nan dama ko arziki da Allah yah ore mata.