Malaman makaranta suna da muhimmanci ga al’umma bayan haka kuma sune ginshikin samar,da ilimi,inda suke gyara yadda tafarkin’yayanmu tun suna kanana yadda za su iya kasancewa a wani lokaci mai zuwa za su, san bi hanyar, da babu wata maganar da nasani.Su masana ilimi ne,su masu bada shawara ne kan abinda yafi dacewa, su masu nuna kan hanyar ko nunawa su ‘yan makaranta masu hanya mafi dacewa ta zuwa inda suka yi niyya,da kuma basu kwarin gwiwa.
Kasancewa matsayin Malamin makaranta lamarin duk ya wuce haka wato shi aikin domin kuwa. Awai bukatar ka bada kwarin gwiwa,ka jagoranta,ka koyar,ka bada misalin abinda ya fi dacewa ayi,ta haka sai Malamin makaranta ya kasance a rayuwar rayuwar shi yaro (dan makaranta tun yana karami har ya kai ga mallakar hankalinsa ba zai taba mantawa da Malamin ba saboda ginshikin rayuwa maikyau daya dora shi akai).
- Yadda Tashar Jirgen Ruwan Apapa-Moniya Za Ta Taimaka Wa Masu Safarar Fitar Da Kaya
- Sin: Idan Har Amurka Na Son Tattaunawa, Ya Zama Wajibi Ta Dakatar Da Aiwatar Da Matakan Gangaci
Lamarin ya zarce maganar cikin aji inda ake koyarwa masu ilimi ko masana lamarin ilimi kamar Malaman makaranta,yadda suke tafiyar da rayuwarsu ta Malanta hakan yana shafar al’ummar da suke zama tare.Ta hanyar dora yara wadanda kan hanyoyi madaidaita da suka dace,Malaman makaranta suna bayar da gudunmawa kan yadda suke dora wadanda aka basu alhakin koyar dasu,domin su san hanyoyin da zasu yi maganin matsalollin da suke damun al’umma.
A wannan mkalar za a duba daliali 12 ko fiye da haka wadanda suka sa Malaman makaranta suna da matukar muhimmanci ga al’umma:
Manyan Ayyukan Malamin makaranta
Malaman makaranta suna da ayyuka wadanda sun fi karfin ayi su a cikin aji saboda wurin ba huruminsu ba ne,abubuwan sun hada da irin kwarewar da suke da ita,wadda za su yi amfani da ita wajen renon/ koyar da daliban da kuma yadda rayuwarsu a matsayin ‘yan makaranatrasu za ta kasance.
Ayyukan Malaman makaranta sun hada da:
Shirya tsarin yadda za a koyar da darussa: Shiryawa da tsara yadda za a koyar da darussa yin hakan ya kunshi ayi abu cikin tsari da lura domin tabbatar da an shirya abubuwa masu amfani wadanda zasu amfani dalibai lokacin da aka koya masu.
Matsayinka na Malamin makaranta idan kana shirin shiga aji koyarwa kamata ya yi tsarin yadda za ka koyar ya yi daidai da manhajar abubuwan da suka kamata a koya masu,ka bayyana dalilan da suka sa za ka koyar da shi darasin,wajen yin amfani da tsare- tsare da suka shafi nau’oin koyarwa daban- daban.
Shirya gabatar ko gudanar da aiki kamar yadda ya dace wata hanya ce da zata bada damar gabatar da aiki kamar yadda ya dace.Muddin dai kana da tsarin yadda za ka koyar a hannunka wanda aka tsara da kan ka hakan zai ja,hankalin wadanda zaka koya mawa su kagara ka koyar dasu,musamman ma kamar yadda ka saba tun farko kana, mai jan hankalin su daliban naka.
Karfafawa dalibai kasancewa ana yin abin tare da su:Matukar kana bukatar ka kasance wanda yake da da’awar koyarwa wadda suma dalibai su kasance ana damawa tare da su/tafiya tare da su,ta yadda su ma, za su san cewa lalle tafiyar tare dasu ake yin ta,sai ta kasance sun saki jikinsu bu wata maganar jin kunya sai su rika bada tasu gudunmawar da kuma musayar ra’ayi.
A, matsayinka na Malamin makaranta za ka iya kara wa wadanda kake lura karatunsu kana iya basu kwarin gwiwa,suma su rika bada gudunmawa inda zaka bude layi wanda zaku rika magana ta samar da fa’idoji na koyarwa,wato kamar yadda zaka raba su zuwa shiyya-shiyya inda zasu rika tattaunawa, da kuma mahawara. Idan ana samun irin hakan a aji yana kara samun sabuwa da karuwa wadda take kara sabuwa da karuwa da ilimi na kowane dalibi.bugu da kari kuma ga yadda kowane dalibi a cikin aji zai ji dadi da kuma gamsuwa a irin hanyoyin da ake amfani da su wajen koya masu,saboda kuwa yana gane abubuwan da ake koya ma sa kwarai da gaske.
Yin bincike da kuma samar da sabbin abubuwan taimakawa koyarwa:Abin so da kauna ne Malaman makaranta koda wane lokaci su zama ma su yin bincike domin su kasance,a cikin kowane hali ake cike kan abinda ya shafi lamarin koyar da ilimi a makaranta suna iya tafiyar da hakan.Matsayin ka na Malami akwai bukatar ka zama cikin yin bincike domin ka bunkasa manhajar abubuwan da za ka koyar domin kar,a same manhajar da ta rasa wasu abubuwan da suka kamata ta kunsa.
Hakanan ma ka na iya amfani da al’amuran fasaha domin ka samar da kayan da za kayi amfani dasu wajen aikin koyarwar ka,ba domin komai ba sai don ka samar da wani hali ko yanayi,hakanan ma ka na iya maida lamarin koyarwar naka abinda za’a rika gani ba sai jiba kadai,ta hanyar yin amfani da dabaru masu yawa na koyar da ‘yan makaranta,wadanda zasu iya nuna lalle gaskiya,a kowace rana ana samun ci gaba wajen amfani da dabaru daban- daban na zamani domin saukaka koyarwa yadda kowa zai iya gane ko fahimtar halin da ake ciki.
Gyara aikin da dalibai suka yi da rubuta duk makin da suka samu:Rubuta makin da dalibi ya samu yana da matukar muhimmaci musamman ma a harkar koyarwa, hakan yana taimakawa sani ko gani irin kwazon da kowane dalibi yake da shi,wannan kuma ya ta’allaka ne kan irin kwazon da ya nuna.
Muddin kana rubuta makin da kowane dalibi tya samu a jarabawar da ka yi masu ko aikin da ka basu, hakan zai baka dama ta yin amfani da hakan wajen bada labarin irin kwazon da kowa yake da shi,ko rashin kokari wanda hakan zai sa,ka san yadda za ka bullowa lamarin.
Idan kana rubuta makin da kowane dalibi ya samu yin hakan zai taimaka maka ajiye da kuma sanin dukkanin kokarin da kowane daga cikinsu ya yi, wanda ta hakan ne za aka iya turwa Iyayensu,su kasance da masaniyar halin da ‘ya’yansu suke ciki a makaranta dangane da abubuwan da ake koya masu.
Samarwa/taimakawa masu koyo da babban taimako: Malaman makaranta suna bayar da taimako wanda kuma ya bambanta domin taimakawa kowane dalibi lamarin da yake nuna cewa kowane dalibi yana da muhimmanci, inda yake da tasa bajimtar,matsalolin da yake fuskanta,da kuma irin yadda ya dace a koyar da shi. Duk idan aka ba kowa taimakon daya kamace shi wannan kuma ana yin hakan ne domin kowane dalibi ya kai irin kololuwar da zai iya kai wa daidai da bukatar sa.
Matsayin ka na Malami kana iya ganewa da kuma gane bukatar musamman ka kowane dalibi da ta shafi yadda za’a koya ma sa, da irin salo- salon da za’ayi amfani da su,kayan da za’ayi amfani da su, domin su gamsar da koyarwa ta musamman da kuma irin kokarin na daliban.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp