Jarabawa wata babbar abu ce mai muhimmanci a rayuwar dalibi saboda tana bada sakamako nau’i biyu ko dai ayi nasara ko akasin.Samun nasarar cin jarabawa wani abin farinciki ne a rayuwar dalibi haka yayin da rashin nasara wani babi ne mai dugunzuma rayuwar shi dalibin,dalilin da ke bada gudunmawa ga rashin samun nasara shine raganci ko ragantaka.Ta wani bangaren ma dalibi ya rika ganin ai shi kamar ma ya samu nasarar ne ko rashin nuna mai da hankali kana bin da ya dace.
Wasu dalibai sun amince da dalilan yayin da wadansu ke ganin ai laifin wasu ne kamar Malamansu, Iyaye,ko kuma Abokai.Su kan ce “Malamai basu koyarwa kamar yadda ya dace” ko “Jarabawa tana da wuyar a samu nasara”sai dai maganar gaskiya idan ba a samu sakamako mai kyau ba wannan na nuna dalibin bai mai da hankalin shi kan maganar yadda za iyi karatu ko shirin da za isa ya ci jarabawar ba.
- Za Mu Nome Dazuka Don Magance Matsalar Tsaro A Neja – Bago
- Shirin Twitter Space Na LEADERSHIP Hausa: Gaskiya Ta Bayyana Kan Bullar Mata Masu Shan Jini
Ganin laifin wasu saboda rashin samun nasara ba magana bace da za a amince da it aba, domini dan baka yi nasara ba saboda yadda Malaminka yake koya ma,to ta yaya sauran dalibai suke cin jarabawar?
Manyan dalilin da suke taimakawa wajensamun nasara sun bambanta da abin da muke tunani,ga dalilan suke sa dalibai rashin samun nasara a jarabawa.
1-Ragonci:
Wannan shine babba daga jerin abubuwan da suke sa rashin samun nasara. Ragonci yana nufin Malaminka zai baka aiki,ka yi rubutu,ko sauran ayyukan da zaka yi a gida domin ka shirya,amma sai dalibi ya sa ragonci a zuciyarsa ya yi ayyukan da aka ba shi.
Wasu dalbai ba su yin rubutu wanda Malami yake yi a aji yayin da wasu ma ba su son su rika zuwa aji, suna gani abin da akwai wuya su zauna su rika sauraren abubuwan da Malamansu suke son koya masu.
Suna bada dalilan da babu makama domin su guje wa yin abubuwan,suna iya kauce ma hakan duk kuwa da yake sun san hakan na iya kai su ga rashin nasara a aji, su kasance raggaye su manufar su ke nan.
Mafita
A yi kokari ayi aiki a lokacin da ya kamata ko wace rana a samu karanta littattafai daban daban domin a samu kara fadada ilimi.
2-Tunanin za a ci jarabawa ko ba ayi karatu ba
Dalili na biyu mai taimakawa wajen rashin samun nasara a jarabawa shi ne a rika Kallon ai an san abu don haka ana ganin ko ba ayi karatu ba ai ana iya samun nasara lokacin jarabawa.”Ko da yaushe mun san mutum ya ga cewar sai yayi karatu zai iya yin karatu domin ya samu nasara”da kuma yadda irin tunani na aniya komai ko ba ayi karatu za a iya samun nasara hakan ke sa ayi karo da rashin nasarar.
Amsa ita ce tabbacin za a iya karatu hakan ke sa a maida hankali babau wani al’amarin wasa sai an samu nasarar cin jarabawa.Ta daya bangaren kuma ganin an san abu don haka ko ba ayi karatu ba za a iya samun nasara wannan ba magana bace mai makama.
Ganin cewa lalle ana iya samun nasara lokacin jarabawa bai kamata dalibai su dauki darasi daya ba su yi tunanin za su iya samun nasara akan wani darasi daya, shi yake saw a su yi watsi da sauran darussan wanda irin hakan ne suke karewa ga iya dana-sani lokacin d suka ga lalle sun fadi sauran darussan a jarabawa,wanda irin hakan ne ke samar da hanya ta ayi rashin nasara.
Mafita
Kamata ya yi dalibi kar ya bada wata hanya da zata nuna ma shi har akwai wani abu da ba zai iya ba,ya dace ya rika koyon sabbin abubuwa.Ya mai da hankali kan darasin da yafi sha’awa,sai dai duk da hakan akwai bukatar ya kara koyon wasu abubuwa saboda ya samu hanya ta samun nasara akan jarabawar da yake ganin ko ake ganin a kalla zai iya samun nasara lokacin jarabawa.