12. Rashin bin dokoki
Akwai hanyar da za abi domin amsa duk tambayar da aka yi lokacin jarabawa said ai dalibai suna fuskantar matsala wajen karantawa da gane yadda tambayoyin suke ballan tana su bada amsoshin da suka kamata.
Alal misali idan tambayar ta bukaci ka rubuta abubuwan da aka bukata daganan kuma ka yi bayani,kana iya rasa wasu abubuwan da ka iya taimaka makai dan tun farko baka baka rubuta abubuwan ba tun farko kafin ka yi bayan a kan kowane daga cikinsu
Koda- yaushe akwai muhimmin abinda ake son ka maida hankalin ka shi za ka yi kamar yadda aka bukaci dalibi ya yi.
Mafita
Kafin ka rubuta amsa ka tabbatar da ka gane tambayar da aka yi ma sosai.
13-Rashin daukar matakin da ya dace
Yawancin dalibai suna fuskantar da shiga dakin jarabawa ne ba tare da sanin yadda za su fuskanci tambayar da aka yi ba,saboda kuwa kowace jarabawa akwai lokacin da ake ware mata.Ana iya faduwa jarabawar idan har ba a san lokacin da za a ware ma kowace tambaya ba.Su tunaninsu shine ko ma na iya tafiya kamar yadda aka tsara shi,ta haka shi ke sa su samu matsala wajen amsa tambayoyin da aka yi ma su lokacin jarabawa.
Mafita:
Ku tambayi Malamanku hanya mafi dacewa da zaku ware ma ko wace tambaya lokacin da za ku amsa ta.
- Rashin koyo kamar yadda ya dace
Bai kamata a shiga aji a sauraren lacca sannan kuma a barta a ajin wsu daliban suna faduwa jarabawa ne saboda basu kwatanta abinda aka koya masu ko suka koya a makaranta.
Ka manta da abubuwan da ka karanta ko aka koya maka a cikin aji saboda kana da wasu abubuwa kamar abokai, yin hira, da sauran abubuwa, haka ne ke sa dalibai faduwar jarabawa.
Mafita
Koyon abinda aka koya ma ko wace rana a matsayinka na dalibi yana kara maka kwarin gwiwa wajen samun sakamako maikyau idan ka rubuta jarabawa.
- Rashin abincin da ya dace
Kana karatu ko nazari lokacin da kake jin barci haka ne? wannan ba haka bane saboda dalibai wadanda suke da matsalar abinci managarci suna samun matsala kwarai da gaske domin da zarar sun gama cin abinci sai bacci ya kama su.Dalibai abinda ya dace dasu shine su Kasane babu kasala tare da su domin su koya kamar yadda ya dace domin sus amu nasara wajen jarabawa.
Mafita
A yi kokari a samu cin nau’in abincin daya dace domin su kasance cikin kuzari.
- Neman shawarwari masu yawa
Shawara tana dakyau amma sai ka dauke ta daga mutum daya amma samun shawara daga wurin mutane da yawa,wannan na nuna ana iya haduwa da rashin sanin makama.
Dalibi ya dace ya yi amfani da shawarar wanda ya san yana sa shi a hanya maikyau domin ya zama mutumin kirki a gabal ko Malamin da yake koya ma shi darasi.Sai dai kuma idan yace zai yi amfani da shawarar kowa hakan na iya daure ma shi kai abinda za isa ranar jarabawa ya rubuta shirme.Hakan kan samar da rashin nasara bayan rubta jarabawa da shi dalibin ya yi.
Mafita
Ka bi shawarar Maigidanka ta yadda za kayi karatu ko koyon wani abu kamar yadda ya kamata.