Masana tattalin arziki da kwararru a bangaren hada-hadar kudi a Nijeriya sun yi bayanin dalilan da suke janyo har yanzu al’ummar Nijeriya ke fama da talauci da fatara duk kuwa da cewa a ‘yan watannin da suka gabata tattalin arzikin kasar (GDP) ya karu da kaso 3.46 a zango na uku na shekarar 2024.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da daraktan kididdiga na tarayya, Adeyemi Adeniran Adedeji, ya sanar a ranar Litinin cewa tattalin arzikin Nijeriya ya fadada zuwa da kaso 3.49 a zango na uku na 2024 daga kaso 3.19 a zango na biyu na 2024.
- IPAC: Tasiri Ko Rashin Tasirinta A Siyasar Nijeriya
- Nijeriya Na Buƙatar Naira Tiriliyan 1 Don Kawo Ƙarshen Cin Zarafin Mata –Bankin Duniya
Bangarorin da suka taimaka wajen karuwar tattalin arzikin Nijeriya sun hada da sashin ayyuka, cibiyoyin hada-hadar kudade, kamfanonin sadarwa, noma, sufuri da kuma bangaren gine-gine.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta wata sanarwar da kakakinsa Sunday Dare, ya nuna gayar farin cikinsa kan ci gaban da tattalin arzikin cikin gida ya samu. Inda ya misalta hakan da cewa zai kara kyautata tattalin arziki.
Sai dai kuma duk da karuwar lambobin a bangarorin, wannan lamarin bai nuna wani tasiri ga rayuwar al’ummar Nijeriya ba. A zahirance dai, ‘yan Nijeriya na fuskantar hauhawar farashin kayayyakin masarufi, wanda ya kasance kaso 33.87 da kaso 39.16 a watan Oktoba. Hauhawar farashin na ta da wa al’umman kasa hankali da jefa su cikin matsin rayuwa.
Da yake maida martani kan wannan matakin a hirarsa da ‘yan jarida, tsohon shugaban majalisar cibiyar kwararrun ma’aikatan banki (CIB), Farfesa Segun Ajibola, ya ce, akwai bambanci tsakanin ma’aunin tattalin arziki da kuma halin zahiri da al’umma ke ciki.
Ya ce karuwar GDP bai wadatar ba wajen samar da yanayin kyautata tattalin arzikin jama’a. A cewarsa, rashin kyan tsare-tsaren da suke akwai su ne suka sabbaba ake samun nakasu daga sauya tattalin arziki zuwa saukaka rayuwa ga jama’a.
“Akwai bambanci sosai wajen shigar da tattalin arzikin Nijeriya zuwa amfanun rayuwar al’umma. Inganta ma’aunin tattalin arziki dole ne, amma babu isassun yanayin inganta walwalar tattalin arzikin jama’a.
“Alkaluma irinsu bunkasar tattalin arziki, ajiyar kudaden waje, rabon bashi, da dai sauransu, sun kafa hanya da samar da ingantacciyar rayuwa ga mafiya yawan marasa karfi a kasa kamar Nijeriya.
“Nijeriya na ci gaba da shaida ci gaba duk da cewa ana samun canjin daga shekarun 1970, amma yawancin jama’a su na fama da talauci saboda rashin daidaito da rashin kyawawan tsari.”
Shi ma babban daraktan cibiyar habaka harkokin kasuwanci masu zaman kansu (PPE), Muda Yusuf, ya ce karuwa GDP ci gaba ne mai ma’ana ga kasar, sai dai ya nemi gwamnati da ta bijiro da tsare-tsaren da suka dace da za su inganta walwalar jama’a.
Kazalika, babban jami’in ‘SD & D Capital Management,’ Mista Idakolo Gbolade, ya ce kididdigar sam ba ta yi daidai da yanayin hauhawar farashin kaya da ake fuskanta ba.