ALIYU ISHAK MU’AZU, tsohon dalibin Jami’ar Maryam Abacha American Unibersity da ke Maradi a jamhuriyyar Nijer ne, a wannan tattaunawar da shafin kimiyya da fasaha ya yi da shi, ya shaida dalilansa na kirkirar manhajar sada zumunta na Afrister. Ya ce, manhajar da ya kirkira tana da manufar taimaka wa mutane wajen sada zumunta a fadin duniya kuma mutane za su samu damar tura sako sannan zai iya zama mai kirkira da zai rika wallafa ayyukansa da na kasuwancinsa. Manya da masu kananan sana’o’i za su iya tallata kayan sana’arsu. Kazalika ‘content creators’ ma za su iya bayyana fasaharsu da ayyukansu da suka yi. Ga yadda hirar ta kasance.
Da farko za mu so ka gabatar da kanka?
Da farko suna na Aliyu Ishak Mu’azu. Na shiga makarantar Maryam Abacha na Nijer a 2020 na kuma kammala a 2023.
Me ka karanta a Jami’ar?
Na karanci kimiyyar kwamfuta (Computer Science).
Yaushe ka kirkiri wannan manhajar ta ka?
A lokacin ina aji biyu (mataki na 200), a lokacin ne na yi tunanin na kirkiri wani abu da kaina sai na fara tunanin me ya kamata na kirkira wanda zai zamanto a ce yau ga shi na kirkiri wani abu. Sai na yi tunanin na kirkiri manhajar sadarwa wanda muka sanya wa suna da ‘Afrister’. Shi dai wannan manhajar-manhaja ce ta sada zumunta. Mutum zai iya tura sako sannan zai iya zama mai kirkira da zai rika wallafa ayyukansa da na kasuwancinsa. Manya da masu kananan sana’o’i za su iya tallata kayan sana’arsu. Kazalika ‘content creators’ ma za su iya bayyana fasaharsu da ayyukansu da suka yi. Wannan shi ne dalilin da ya sa na kirkiri wannan manhaja ta ‘Afrister’.
Lokacin da ka samar da wannan manhaja din; akalla mutum nawa suke bin ku a wannan manhaja din?
Yanzu akalla gaskiya muna da mutane sama da dubu goma. A hakan din ma ba mu yi wani talla ba. Amma insha Allahu mun dan saka ne domin mu ga ya ya ra’ayoyin mutane a kan manhajar. Sai muka ga mutane sun karbi manhajar sosai. Alhamdulillahi kwanan nan muna sa ran za mu samu mutane sama da dubu dari idan muka tallata wannan manhajar.
Me ya ba ka sha’awa ka samar da wannan manhajar?
Gaskiya abin da ya ba ni sha’awa na samar da wannan manhajar shi ne; na duba tarihi ne sai na ga wanda ya kirkiri Facebook shi ma din ya kirkiri Facebook din ne a lokacin da yake jami’a. Sannan kuma na ga cewa mu nan Afrika musamman mu nan Nijeriya haka kuma Arewacin Nijeriya an bar mu a baya bangaren kirkira, to sai na ga cewa ya kamata a ce na yi wani abu wanda zan zamanto na sanya makarantarmu ta zama abin alfahari, sannan kuma na sanya Nijeriya da Afrika ta zama abin alfahari.
Ya zama a ce yau ga wani dan Afrika dan Nijeriya kuma dan Arewa ya kirkiri wani abu babba haka. Shi ne burina da ya sanya na kirkiri wannan manhaja. A takaice dai kalubale ne ga dan Afrika ko na cewa dan Nijeriya ko dan arewa wajen ganin mun shiga an dama da mu wajen kirkire-kirkire da zai taimaka da kuma fito da sunan kasarmu, yankinmu da nahiyarmu a duniyance.
Daidai lokacin da kake kirkirar wannan manhaja, ga shi kuma lokacin da shi shugaban makarantarku Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo yana matashi kamar ka ya samar da wannan jami’a. Wani samfur kake dauka a rayuwarsa?
Gaskiya Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo jagora na ne sosai. Duba da yanayin yadda yake gudanar da rayuwarsa da yadda yake da kwazo, na ce gaskiya zan kwaikwayi yadda yake gudanar da rayuwarsa. Yana daga cikin dalilin da yasa na kirkiri wannan manhaja. Sannan kuma ya ba ni gudummawa sosai. Yana daga cikin gudummawar da ya ba ni ya sanya ma manhajar ta kai iwarhaka. Kuma gaskiya ba ni kadai ba, har da wasu da dama da suka yi bajinta a wasu bangarorin na san ya zama musu alami musamman matasa wajen ganin sun cimma burinsu ko kuma sun zama masu amfani a cikin al’ummarmu.
Wani sako kake da shi ga gwamnatin Nijeriya da Afrika da duniya baki daya a kan wannan manhaja?
Sakona ga gwamnatin Nijeirya shi ne cewa; ya kamata a ce duk wani dan Nijeriya da ya kirkiri wani abu wanda ya zamanto abin zai amfani al’umma, to ya kamata a ce su duba abin su taimaka masa. Sannan kuma su yi yadda sauran kasashen ke yi. Misali; shugaban kasar Amurka da na Chana da sauran kasashen suna da wani shiri wanda suke taimakon ‘start ups’. Duk wani ‘start up’ da aka kirkira su kan yi kokari su duba su ga abin da ya dace su taimaki ‘start ups’ din sai ya zamo ‘start ups’ din ya girma. Kowanne start up yana bukatar jagoranci da tallafi da daukar nauyi.
Babban kalubalenmu a yanzu shi ne wanda za su tallafa mana. Saboda da wannan tallafin ne idan muka samu shi ne za mu ci gaba da kula da abubuwan mu har ya zama mun samar da manhajar mai inganci wanda zai zama mutane za su yi amfani da shi suna jin dadi abin ya zo ya habaka.
Mene ne sakonka matasa domin samar da ire-iren abin da ka samar?
Sakona ga matasa shi ne duk wani wanda yake da wani fasaha na wani abu ya yi kokari ya yi amfani da wannan fasahar ta shi ta hanyar da ya dace. Ya yi kokari ya kirkiri wani abu da wannan hazakar ta shi domin ya taimaki al’umma da kan shi. Saboda yanzu zamani ya canza. Kirkira a yanzu shi ne yake kan gaba a kan komai. Kuma ina kira ga gwamnatoci da su taimaka wa dukkanin matasa masu fikira da basira domin ganin kasar ta ci gaba da kuma bai wa wadanda suke da basira damar baje hajasarsu. Wasu da dama suna nan amma sakamakon rashin tallafin yadda za su baje hajasarsu sai ya zama basirar nasu na nan ba tare da an ci gajiyarta ba.
Mene ne sakon ka ga Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo?
Sakona ga Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ita masa godiya musamman na wannan gudummawar da ya ba ni da karfin guiwa da ya kara min. Ina masa gaskiya sosai. Sannan kuma ina rokon Allah ya taimake shi ya daukaka shi. Sannan kuma wannan abin alherin da yake yi wa al’umma da mutane da dalibai musamman a Arewacin Nijeriya, muna rokon Allah ya sa ya ci gaba sannan kuma ya yi fiye da hakan.