Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta jihar Kano ta fara kamun awakin da ke cin bishiyoyin da aka dasa a ƙarƙashin aikin sabunta birane na jihar.
Kwamishinan Muhalli Dr. Dahir Hashim ya bayyana cewa an riga an tsare wasu Akuyoyi a ofishin Ƴansanda na shirya ta ɗaya saboda cin bishiyoyin da aka dasa a manyan hanyoyin birnin.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Masunta 3, Sun Sace Dabbobi A Sakkwato
- NNPP Ta Tafka Asara, Ƴan Majalisa 2 Daga Kano Sun Koma APC
“Mun fara dasa bishiyu a manyan hanyoyi kamar Lodge Road da Race Course don rage zafi da gurbatar iska, tare da ƙawata birnin,” in ji Hashim.
Duk da haka, aikin da aka tsara don dasa bishiyoyi yana fuskantar ƙalubale daga dabbobin da ke yawo a gari.
ya kara da cewa. “Mun samu koke-koke cewa wasu al’umma suna barin awakansu suna yawo, waɗanda ke lalata bishiyoyinmu. Ba za mu yarda da hakan ba – tuni mun tsare wasu awaki”
Kwamishinan ya kira ga al’umma su bayar da gudunmawar su don tallafawa aikin, yana mai cewa awakin da aka kama za a ci gaba da tsare su har sai an gano masu su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp