Shugaban kungiyar manoman masara na kasa Dakta Bello Abubakar Funtua ya bayyana cewa, Masara tan miliyan 12.4 kacal aka iya noma wa kasar, sakamakon matsalolin ambaliyar a wasu sassa na kudu maso-gabas da kuma arewa maso gabas na kasar nan.
Bello ya sanar da hakan ne a wani taron kwararru a fannin na noman Masara da aka gudanar a kwanan baya, inda ya kara da cewa, kazalika karancin taki a wasu sassa na yankankunan, ya kara janyo rashin nomanta kamar yadda ake bukata.
- An Gurfanar Da Wani Mutum Da Ya Kashe Kaninsa Dan Shekara 6
- Gwamnatin Jihar Gombe Na Bai Wa Fannin Noman Auduga Mahimmanci – Kwamishina
“Tan miliyan 12.4 na Masara kacal aka iya noma wa a sakamakon matsalolin ambaliyar ruwa da karancin taki a wasu sassa na yankankunan kudu maso-gabas da kuma arewa ta gabas da arewa ta yamma.”
Ya ci gaba da cewa, a yanzu Nijeriya na samar da Masara ninki goma ne kawai, inda ya kara da cewa, daga 1999 zuwa shekara ta 2019, a duk shekara masarar da ake nomawa a Nijeriya ta na ninkawa sau biyu.
A cewarsa, hakan ya sanya daga 2014 zuwa 2019 Nijeriya ta zama kasa ta biyu kan noman Masara a Afrika, inda take noma Masara tan miliyan 10.8 a duk shekara baya ga Afrika ta Kudu wadda take kan gaba a noman Masara a nahiyar Afrika, da take noma masara tan miliyan 12.9 a duk shekara.
Bello, ya yi bayyana cewa shekara ta 2014 Nijeriya ta noma Masara tan miliyan 10.1 inda a 2015 ta noma tan miliyan 11.6, sai a 2016 da ta noma tan miliyan 11.6, sai shekarar 2017 ta noma tan miliyan 10.4, a 2018 zuwa 2019 ta noma kimanin tan miliyan 11.0.
” Daga 2014 zuwa 2019 Nijeriya ta zama kasa ta biyu kan noman Masara a Afrika, inda take noma Masara tan miliyan 10.8 a duk shekara baya ga Afrika ta Kudu wadda take kan gaba a noman Masara a nahiyar Afrika, da take noma masara tan miliyan 12.9 a duk shekara.”
Bello ya kuma buga misali da cewa, a shekaru biyar na tsohowar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Nijeriya tana noma masara tan miliyan 10.8 a duk shekara.
Ya bayyana cewa, Masarar da Nijeriya ta noma a shekara ta 2019 tan miliyan 12.6 ta yi kasa idan aka yi la’akari da wadda ta noma a shekarar 2020 a sakamakon matsalar karancin ruwan sama,
“Masarar da Nijeriya ta noma a shekara ta 2019 tan miliyan 12.6 ta yi kasa idan aka yi la’akari da wadda ta noma a shekarar 2020 a sakamakon matsalar karancin ruwan sama. ”
A na sa jawabin Darakta Janar na Majalisar samar da iri ta kasa Dakta Philip Ojo, ya nanata mahimmancin akan shuka ingantacce Irin Masara, musamman domin manomanta su samu riba mai yawa.
Ya ce, ya zuwa yanzu an samar da irin shuka na masara daban-daban har 140, don ganin an bunkasa noman Masara a Nijeriya .
” Akwai matukar mahimmancin akan shuka ingantacce Irin Masara, musamman domin manomanta su samu riba mai yawa. ”
Shi kuwa wani kwararre a fannin Mista Joseph Kibaki ya bayyana cewa, akwai bukatar a samar da kyawawan tsare -tsare da shirye shirye, musamman daga bangaren gwamnatin tarayya domin a kara bunkasa fannin noman Masara a daukacin fadin kasar nan.
“Akwai bukatar a samar da kyawawan tsare -tsare da shirye shirye, musamman daga bangaren gwamnatin tarayya domin a kara bunkasa fannin noman Masara a daukacin fadin kasar nan.”
Su kuwa wasu masana a fannin noman Masara a kasar nan sun bayyana wasu hanyoyin da ya dace a dauka domin a kara bunkasa noman Masara a kasar nan.
Sun sanar da hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki a fannin suka gudanar tare da kuma kokarin lalubo da mafita kan kalubalen da fannin ke fuskanta.
Mahalarta taron sun kuma attaunawa kan kalubale da fannin ke fuskanta a kasar nan tare da kuma bayar da shawarwari, musamman ga gwamnatin tarayya kan yadda a lalubo da mafita akan kalubalen.