Kasar Amurka mai rike da Kofin ta fice daga gasar cin kofin duniya ta mata bayan da Sweden ta fitar da ita a bugun fenariti a wani yanayin mai ban mamaki a Melbourne.
Amurka ce ta mamaye wasan a cikin mintuna 120 amma mai tsaron ragar Sweden Zecira Musovic ta hana su zura kwallo a raga.
- Nijeriya Ta Doke Senegal A Wasan Karshe Na Kwallon Kwando Ta Mata
- Ronaldo Ya Jefa Kwallon Da Ta Saka Kungiyarsa Zagayen Gaba A Gasar Zakarun Larabawa
Bayan kammala mintuna 120 na wasan an tafi bugun daga kai sai mai tsaron raga inda yan wasan Amurka uku suka barar da bugun fenareti.
Talla
Ciki har da tauraruwarsu ta kwallon kafa Megan Rapinoe a wasanta na karshe a matakin kasa da kasa.
Sweden za ta kara da Japan a wasan kusa da na karshe.
Talla