Rahoton da Cibiyar Kuɗi ta ƙasa FRC da kuma na Cibiyar Baje Koli ta jihar Legas LCCI bisa hadaka da ƙungiyar tabbatar da ƙima IO domin samar da takardun kasuwanci ga ƙanana da matsakaitan sana’oi MSMEs.
Babban Sakatare na Cibiyar ta FRC, dakta Rabiu Olowo, ya sanar da haka a wani taron bita, musamman domin a lalubo da mafita, kan durƙushewa ƙanana da matsakaitan sana’oi a ƙasar.
Ya bayyana cewa, sama da kaso 50 a cikin dari na ƙanana da matsakaitan sana’oi ke durƙushewa a farko shekarar da suka fara gudanar da kasuwancinsu.
- FRCN Ya Kaddamar Da Shirin Koyar Da Sinanci Mai Taken “Hello China”
- Nijeriya Za Ta Karɓi Baƙuncin Taro Karo Na 4 Na Ƙananan Sana’oi Na Ƙungiyar AU
Taken taron bitar shi ne, gudanar da shugabanci na gari, a matsayin ginshiƙin dabaru, na ɗorewar ƙanana da matsakaitan sana’oi a ƙasar, inda kuma taron, ya samu halartar masu ruwa da tsaki daga ɓangaren gwamnati da kuma na kamfanoni masu zaman kansu.
Olowo ya ƙara da cewa, sama da kaso 50 a cikin dari na ƙanana da matsakaitan sana’oi a ƙasar, na mutuwa ne, a farkon shekarar da suka fara gudanar da kasuwancinsu, inda kuma sama da kaso 95 a cikin dari ba su kai wa koda shekara biyar suna gudanar da kasuwanci, suke durƙushewa.
Ya danganta mutuwar ta ƙanana da matsakaitan sana’oi a ƙasar, kan rashin samun rancen kudaɗen da za su ci gaba da ka kasuwancin su da rashin kayan aiki, da rashin kasuwa da ba a samu sosai da kuma rashin gudanar da ingantaccen shiri, kafin su fara gudanar da kasuwancinsu.
Ya sanar da cewa, ya zama wajibi, ƴan kasuwa musamman ƙanana da matsakaitan sana’oi a su sani cewa, bab wani batun yin wani holewa, na jin daɗi
Ya bayyana cewa, sama da ƙanana da matsakaitan sana’oi 40 a ƙasar nan, burin su ba shi ne, na ƙara yawan adadin alƙaluma ba, anna burin shi ne, na ƙarfafa zurewar kasuwancinsu.
“Alƙaluma sun nuna cewa, akwai ƙanana da matsakaitan sana’oi 40 a ƙasar nan, wanda hakan ya nuna cewa, sun kai kimanin kaso 96 a cikin dari, na kasuwancin da ake yi a ƙasar, inda kuma ake da kaso 84 na masu aikin yi, musamman duba da cewa, fannin na taimaka wa, wajen samar da ayyukan yi da kuma bayar da gudunmawa ga tattalin arzikin ƙasar da ya kai kimanin kaso 48, a duk shekara, ” Inji Olowo.
Ya ci gaba da cewa, wannan sabon tsarin na kasuwacin, zai taimaka wajen cimma samar da tsarin tabatar da ci gaban ƙanana da matsakaitan sana’oin hannu.
“Babu wata hanya da zamu iya cimmma burin samaun dala tiriliyan daya, ba tare da yin amfani da ɓangaren ƙanana da matsakaitan sana’oin hannu,” A cewarsa.
Shi kuwa shugaban Cibiyar ta LCCI,Gabriel Idahosa, ya bayar da tabbacin cewa, Cibiyar za ta bayar da goyo baya domin a cimma wannan tsarin, na samar da takardun shedar gudanar da kasuwancin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp