Wasu makiyaya a Jihar Taraba, sun tabka asarar Shanunsu sama da 1,000, sanadiyyar barkewar wata cuta a yankin Mambilla Filato da ke Karamar Hukumar Sardauna.
Rahotannin sun bayyana cewa, bullar wannan cuta; ita ce mafi muni a tarihin kiwo a yankin.
- Gwamnan Filato Ya Ƙaƙaba Dokar Hana Fita Ta Awa 24
- An Kashe ‘Yan Bindiga Da Dama A Wani Artabu Da Sojoji A Filato
An ruwaito cewa, cutar wadda aka bayyana ta a matsayin mafi hadari ga Shanu, an fara gano bullar ta ne a Kauyukan Dorofi, Mayo Ndaga, Kwarakwara, Leme, Tep, Labare da kuma Furmi a ranar 10 ga watan Yulin 2024.
Akasarin Fulani da sauran kabiliun da ke zaune a yankin na Mambilla Filato, makiyaya ne, wadanda ke killace Shanusu ba tare da barin su suna fita kiwo ba. An rawaito cewa, daya daga cikin masu kiwo a yankin; Alhaji Abbas Yabuba na cewa, wannan shi ne karo na biyu da masu kiwon suka yi asara a cikin kankanin lokaci na Shanu da dama sakamakon bullar wannan cuta.
Ya kara da cewa, a wannan karon cutar ta bulla ne a yankuna shida, ta kuma munana matuka; domin akwai mai kiwo daya, da ya yi asarar Shanu kimanin 80, sai kuma dai-daikun makiyaya da suka yi asarar Shanu daga 50 zuwa 60.
Sai dai ya ce, daukin gaggawar da suka samu daga ma’aikatar aikin gona ta jihar, na zuwa duba lafiyar Shahun, ta taimaka matuka wajen dakile yaduwar cutar.
Shi ma wani makiyayin, Adamu ya kiyasata asarar da masu kiwon suka yi sakamakon bullar cutar, inda ya ce ta haura sama da ta Naira biliyan uku.
Har ila yau, an ruwaito Daraktan duba lafiyar dabbobi na ma’aikatar aikin gona ta jihar, Dakta Francis Nathan ya sanar da cewa, an girke jami’an duba lafiyar dabbobi a shalkwatar Gembu ta Karamar Hukumar Sardauna, don kai wa ma’aikatar rahoton barkewar cutar.
Ya ci gaba da cewa, an samu magunguna da Allurai daga cibiyar binken lafiyar dabbobi ta kasa, Bom da ke Jihar Filato, don yi wa Shanun rigakafin cutar. Ya ce, sun yi hanzarin zuwa yankunnan da cutar ta barke tare da fara duba lafiyar Shanun da suka kamu da cutar, inda ya kara da cewa, Shanu sama da 500,000 aka duba lafiyarsu tare kuma da yi musu allurer rigakafi.
Har ila yau a cewar tasa, ana matukar samun shigowar makiyayan Shanu daga Kasar Kamaru zuwa cikin Karamar Hukumar Sardauna, haka nan mu ma namu na shiga kasar yin kiwo, inda ya sanar da cewa, dakatar da shigar Shanun ne kawai zai sa a dakile yaduwar cutar.
Haka zalika, wani bincike ya nuna cewa; duk da dimbin yawan dabbonin da ake da su a yankin na Mambilla Filato, duk dakin duba lafiyar dabbobi daya; likitan daya ne, duba da yadda aka kiyasata cewa, a Karamar Kukumar ta Sardauna akwai Shanu kimanin miliyan biyu da ake kiwatawa.