Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, a yau Alhamis ya bayyana cewa dakatar da tsohon Gwamnan babban Bankin Najeriya (CBN), Muhammad Sanusi II, ya faru ne saboda wasu laifukan kuɗi ba don batun zargin batan kuɗi da yayi ba.
Jonathan ya bayyana hakan ne a Abuja yayin ƙaddamar da wani littafi da tsohon Ministan Kudi, Dr. Shamsudeen Usman, ya rubuta mai suna “Public Policy and Agent Interests: Perspectives from the Emerging World.”
- EFCC Ba Ta Taba Gayyato Ni Gabanta Ba – Jonathan
- Kabilanci Da Magudin Zabe Ke Kassara Samun Shugabanci Nagari – Jonathan
Jonathan ya musanta ikirarin Muhammadu Sanusi na cewa an dakatar da shi ne saboda ya fallasa zargin batan $49.8 biliyan daga asusun gwamnatin tarayya. Ya yi bayanin cewa an dakatar da Sanusi ne bayan tambayar da kwamitin rahoton kudi na Nijeriya (FRC) ya yi kan wasu kashe-kuɗaɗen da ba su dace ba a CBN. Jonathan ya ƙara da cewa, “Akwai matsalolin da suka dace a bincika.”
Tsohon shugaban ya kuma musanta zargin cewa Nijeriya ta rasa wannan adadin kuɗin a lokacin mulkinsa, yana mai cewa kasafin kuɗin ƙasar a wancan lokacin bai wuce ya kai $31.6 biliyan ba kawai, don haka ba zai yiwu a ce $49.8 biliyan sun bace ba tare da an lura ba.
Jonathan ya jaddada cewa bayan binciken kuɗi na PwC, an gano cewa $1.48 biliyan ne ba a bayyana ba, kuma an umurci kamfanin NNPC da ya biya wannan kuɗin cikin Asusun Tarayya. Ya kuma bayyana cewa binciken majalisar dattijai bai gano shaidar batan miliyoyin kuɗaɗen da ake zargi ba.
Sanusi, wanda ya halarci taron, ya mayar da martani cikin raha, inda ya kira Jonathan da “Ogana wanda ya kore Ni,” amma Khalifa ya zaɓi ƙin yin tsokaci kan batun. Maimakon haka, ya ja hankalin ƙasar kan amfani da Matatar man fetur ta Dangote yadda ya kamata tare da kauce wa duk wani cikas ga ci gabanta.
An kuma ƙaddamar da Cibiyar Shamsudeen Usman Foundation da kuma wani taron neman taimakon kuɗi don ƙirƙirar Cibiyar Fasahar Artificial Intelligence a yayin taron.