Tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jagoran jami’yyar NNPP na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana dalilan da suka sanya har yanzu yake tsoma baki a tafiyar da gwamnatin jihar mai ci.
A cewar Kwankwaso, yana tsoma bakinsa ne a tafiyar da gwamnatin domin komai ya tafi yadda ya kamata a shugabancin jihar, inda ya kara da cewa, ya kuma yi hakan ne, don a yi aikin tafiyar da jihar cikin tawaga daya.
- An Cafke Tsohon Kwamishinan Ganduje Kan Zargin Badakalar Biliyan 1
- Gwamnatin Sakkwato Ta Kafa Kwamitin Binciken Mukaman Karshe Na Tambuwal
Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan Rediyon RFI ya yi da shi, inda Kwankwaso ya ce, abin da mutanen jihar a yanzu suke son gani shi ne fara gudanar da aiki a jihar.
A cewarsa, “mu tawaga daya ce, kuma duk bita da kullin da ‘yan adawa suke yi mana don su karkatar da hankalin gwamnatin jihar mai ci a yanzu, ba za su samu nasara ba.
Ya ce, “Rusau da muke yi a Kano gyara muke yi kuma wani abu ne da aka faro shi tun a 2019; wanda kuma duk wani gwamna da ya yi wani gini a makaranta ko a Masallaci ko kuma Badala, ba za mu lamunci hakan ba.”
A cewarsa,“A duk fadin duniya babu wani tsari da ya ce a rusa Jami’a ka gina shaguna, a tsawon shugabancin jihar Kano da na yi na shekaru takwas ban taba bai wa wani ko kafa daya ba don ya yi gini a Firamare ko a Jami’a ba.”
Kwankwaso ya ci gaba da cewa, “Mun kirkiro bude sabbin wurare a Kano, kamar su Kwankwasiyya, Danladi Nasidi da sauransu wadanda kuma duk mun biya diyya, amma mutane suna fatan mu rusa gidajen mu biya su diyya.”
A cewarsa, “Duk bayanan na nan a ajiye, ban taba bai wa kowa ko da kafa daya ta wani fili a Badala ba kuma ban mallaki komai a can ba haka ban umarci wani, ya bai wa wani ba.”