Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya nada tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Attahiru Muhammadu Jega, a matsayin mai ba shi shawara ta musamman, kuma mai kula da shirin samar da sauyi a fannin kiwo.
Bayo Onanuga, mai magana da yawun shugaban kasa, ya tabbatar da nadin na Jega a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a da ta wuce.
- Kalaman Lai Chin-te Na Shan Suka A Fadin Taiwan
- NPA Za Ta Yunkuro Don Zamanantar Da Ayyukan Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya – Dantsoho
Sanawar ta ce, Tinubu ya yi fatan nadin na Jega, zai kawo ci gaba a harkar noma da kiwo, tare da karfafa yunkurin raya kasar.
Kafin wannan nadin na Jega, ya kasance mataimakin shugaban kwamitin shugaban kasa kan samar da sauyi a bangaren noma da kiwo tare da shugaban kasar Bola Tinubu.
Kazalika, kwamitin ya gabatar da shawarwari masu muhimmanci kan yadda za a inganta fannin aikin noma da kiwo da kuma kafa ma’aikatar bunkasa kiwon dabbobi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp