Wasu kwararru a fannin kiwon dabbobi, sun yi kira ga Ma’aikatar Bunkasa Kiwon Dobbobi ta Kasa, da ta kafa cibiyoyin da za a rika gudanar da bincike, kan nau’ikan dabbobin cikin gida a shiyoyi shida na fadin kasar nan.
Sun yi kiran ne, a karkashin kungiyar masu kiwon dabbobi ta kasa (NSAP).
- APC: Ko Sadaukarwar Ganduje Za Ta Dakile Barazanar Jam’iyyun Adawa A Zaben 2027?
- Kayayyakin Sin Na Kara Samun Karbuwa A Kasuwar Duniya
Kiran nasu, sun yi shi ne a taron kungiyar karo na 50 na kasa da ya gudana a Jami’ar Tarayya da ke a garin Lafia, ta Jihar Nasarawa.
Kazalika, kungiyar ta yi nuni da cewa; akwai bukatar a rika taimaka wa cibiyoyin da ke gudanar da bincike kan dabbobi, musamman ta hanyar gudanar da yin bita a kai-a kai da tarurruka, wanda kuma za a rika gudanar da tarukan tare da masu bincike kan fannin dabbobi da masu samar da tsare-tsare.
Shugaban Jami’ar ta tarayya da ke garin Lafia, a Jihar Nasarawa Farfesa Shehu Abdul Rahman ne, ya bude taron.
Taken taron shi ne: “Bunkasa Fannin Kiwon Dabbobi, Domin Samar Da Wadataccen Abinci Da Bunkasa Tattalin Arzikin Kasa”.
A cikin sanarwar bayan taron da Shugaban Kungiyar Farfesa Olaniyi Babayemi da kuma Sakatarenta, Dakta Folasade Jemiseye suka sanya wa hanu, sun jaddada bukatar da a rungumi yin kiwon dabbobi ta fasahar zamani, domin a rika samar da nau’ikan dabbobin da ake kiwatawa a fadin wannan kasa.
A cewar sanarwar, akwai kuma bukatar a samar da tsarin kula da dabbobin da yadda za a rika ciyar da su da kuma sanya ido a kansu, domin kare su daga kamuwa da cututtuka.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, akwai kuma bukatar a samar da dabbobin da ke iya jurewa sauyin yanayi, sannan kuma mahukunta su kara bai wa masu kiwon dabbobin kwarin guiwa, a kan mayar da hankali domin yin kiwo tare da samar wa da masu kiwon ingantattun kayan aiki, kuma na zamani.
“Akwai bukatar masu ruwa da tsaki a fannin kiwon a kasar nan, su karfafa wa matasa guiwa, wajen rungumar yin kiwo domin samun riba da kuma samar musu da kwarewa da kuma ba su horo, wanda hakan zai sanya a cimma burin da kasar ta sanya a gaba na kara habaka fannin kiwo a kasar”, in ji sanarwar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp