A ranar Talata (28 ga Nuwamba, 2023) ne na hadu da wani arashi a kafar sadarwa ta zamani, inda na yi kacibis da wani bidiyon Sanatan Kano ta Kudu, Kawu Sumaila, yana jan-hankali ga “yan siyasar jihar Kano musamman, don a kauce wa munana zato ga bangaren alkalai su kadai, tare da nuna cewa su ne kadai kanwa uwargami, game da rincabewar lamuran siyasa a Nijeriya, musamman ma a Kano, duba da irin danbarwar shari’un kujerar gwamna da ake ta fuskanta a yau. Arashin shi ne, marubucin, na da niyyar dan tofa wani abu makamancin wannan, a rubutun namu na wannan Sati.
Duk da cewa, wannan marubuci bai kai ga kallon wancan faifan bidiyo daga farko zuwa karshe ba, amma daga abinda ya ji, Sumailan, ya nuna tsakanin Alkalai da “yan Siyasa, kowa na da irin nasa laifi, ya ma fi kaurara ko jingina laifin akan “yan’uwansa “yan siyasa, musamman idan za a yi duba da irin yadda suke damalmala lamuran siyasa da sauran janibobi ko sinadaran dimukradiyya a Nijeriya, faro tun daga matakin zaben cikin gida na jam’iyyu, tafi tafi har zuwa kan zaben du-gari da makamantansu.
- Shugaban Kasar Sin Ya Jaddada Muhimmancin Raya Yankin Delta Na Kogin YangtzeÂ
- Ba Zan Yi Katsalandan A Gwamnatin Ododo Ba – Yahaya Bello
A lissafi da hasashen wannan marubuci, kashi tamanin (80%) na bantarewar al’amudan dimukradiyya a wannan lokaci a Kano da ma Kasa bakidaya, za a dora shi ne kacokan akan “yan’uwan Kawun, wato “yan siyasa. Duba da yanayin rikita-rikitar hukunce-hukuncen shari’un zabe da ake dambarwarsu a yau, da ace jam’iyyun siyasun, da kuma lauyoyinsu, za su rika yin abin da ya dace, na dabbaka Doka da Oda, to da babu shakka, sai kusan kashi tamanin da biyar (85%) cikin dari na kwamacalar shari’un da ake gabatarwa mabanbantan Alkalai, faro tun daga Kotun Saurarar Korafe Korafen Zabe, Kotun Daukaka Kara da Kotun Koli sun ragu matuka da gaske.
Ba za mu bazama cikin tarihin siyasar Kasar ba, duba da zurfin bayanai ko misalai da ke jibge karkashin wannan tsokaci, illa-iyaka, za mu dan tsakuro wasu abubuwa ne da suka faru cikin wannan Jamhuriyar Siyasa ta Hudu da muke ciki a yau, wadda ta faro tun daga Shekarar 1999 zuwa yau (2023). Kadan daga wasu abubuwan da jam’iyyun siyasun suka kware akai, sun hadar da gabatar da zabukan cikin gida na jam’iyya bisa tsantsar son zuciya; murguda tsarin mulkin jam’iyya don gamsar da shugabanni; kin bin umarnin kotu; kawo shubuha a kundin dokar zabe; amfani da kotuna; kashe manyan abokanan hamaiyar siyasa da sauransu.
Zaben Cikin Gida Na Jam’iyyu “Primary Elections”
Kamar yadda kowane dan Nijeriya ya kwana da sanin cewa, tsarin mulkin kowace jam’iyya a wannan Kasa, ya yi alkawarin zai gudanar da zabukan cikin gida bisa yadda tanadin Tsarin Mulkin Kasa ya nusar.
Yaya jam’iyyun siyasa a wannan Kasa ke gudanar da zabukan na cikin gida a yau? Saboda mummunan son zuciya da a yau ake aiwatarwa cikin irin wadancan zabuka, ta kai ta kawo, a manyan jam’iyyun Kasar, karfin makudan kudade da dan takara ke da shi, ko karfin wata kujerar mulki da yake akai, koko wani bajimin ubangida na siyasa da yake da, koko wani mai karfin mulki ko kudi ko karfin fada aji cikin jam’iyya da ya tsaya masa, an wayigari, wadannan irin dalilai da makamantansu ne kadai ke sanyawa a kai ga nasarar lashe irin wadancan zabuka!!! Irin wancan son zuciya a cikin zabukan ne suka yi sanadiyyar ruguje da daman zabukan na cikin gida a wasu Kotunan Shari’ar Kasar, dab da fara gudanar da Zaben Shekarar 2011 a wannan Kasa.
Waye bai san irin tsantsar son zuciyar da aka gabatar a zabukan cikin gida na jam’iyyar CPC ta Baba Buhari a nan Kano ba cikin Shekarar 2011? Daga wannan lokaci ne ma ai Ahmadu Haruna Zago ya kara kaurin suna a siyasar Kano. A karshe dai jam’iyyar CPCn ta tunkuyi burji ne nan take saboda son zuciyar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar!!!. Me ya kawo dalilin kwace kujerar gwamnan APC a bai wa jam’iyyar PDP a Zaben Shekarar 2019 a can jihar Zamfara? Da jam’iyyun siyasar sun yi zabukan cikin gida bisa gaskiya da adalci, zai kai ga kwace kujerar gwamnan na Zamfara a Zaben 2019 da aka gudanar? Da jam’iyyun siyasun na yin adalci a zabukan, shin, zai kai ga Kotuna su ruguje akasarin zabukan cikin gida da aka gudanar a Shekarar 2011? A tunaninka mai karatu, ashe jam’iyyun siyasun, ba su ne ke fara bude kofofin da Kotunan Kasar za su rika yi musu kwab-daya ba?
Murguda Kundin Dokar Zabe
Sau nawa ne a wannan Kasa, za a ga “yan Majalisun Taraiya na kokarin murguda Kundin Dokar Zabe, kawai don ya biya musu irin bukatunsu na kashin-kai, musamman na son dauwama bisa madafun-iko har abada!.
(Source, December 6, 2010 & M. Anwar, 2014 : 216).
Me ya kawo mummunar danbarwa da samun tufka da warwara a Kotunan Shari’un Zaben Shekarar 2003, in ba miyagun son zuciyar da “yan siyasa suka turbuda a cikin Kundin Dokar Zabe na 2002 ba!.
Ko an manta lokacin da wasu daga Majalisun Wakilai da na Dattijai masu kishin Kasa, mutane irinsu Patrick Obahiagbon da Andrew Uchendu da Ita Enang da sauransu suka yi kundubala tare da baje mummunan yunkurin takwarorinsu na Majalisa, tare da kawo karshen yin kwaskwarima da aka tasamma yi, a sashi na 87 na Kundin Dokar Zaben 2010, kawai don amfanar da kawunansu sabanin al’umar Kasa!
(Source, December 6, 2010 & M. Anwar, 2014 : 217).
Shi ma irin wancan lugwigwita Kundinan Dokokin Zabukan Kasar, alkalai ne ke yi? Zabuka nawa ne ake tarwatsawa a Kotunan, sakamakon rika-rikitar da take kunshe cikin irin wadancan Kundayen Dokokin Zaben a Kasar?
Murguda Tsarin Mulkin Jam’iyya
Duk da cewa, rashin dabbaka tsarin mulkin jam’iyya a zaben cikin gida na jam’iyyu tamkar yadda aka gabatar da misali a baya, na iya jazawa jam’iyya rasa kujerarta, ko da kuwa ta samu galaba a babban zabe na Kasa, hakan bai sa jam’iyyun siyasun shiga taitayinsu ba, a jiya da yau. Da za mu yi dan duba kadan baya cikin zabukan wannan Kasa, misali, Zaben Shekarar 2007, za a yi kwalli da wurare da dama inda aka sami jam’iyyu na yin wurgi da tsarin mulkin jam’iyya a zabukan fid da gwani na jam’iyya.
Bayan jam’iyyun sun ki dabbaka ka’idojin tsarin mulkin nasu, wani abin takaici da kaico shi ne, ko da Kotunan Shari’a sun ja hankalinsu na su gyara, sai su yi mursisi abinsu. Sai aka wayigari cin amanar dan jam’iyyar da ba shi manya suke so ya sami nasarar lashe zabe ba, wani abu ne mai saukin gaske.
A jihar Yobe a zaben Shekarar 2007, ta tabbata cewa, marigayi Sanata Usman Albishir ne wanda ya sami nasarar lashe zaben cikin gida na kujerar gwamna karkashin inuwar jam’iyyar ANPP, amma, sai jam’iyyar tasa ta mika nasarar wannan takara da ya samu zuwa ga Sanata Mamman Bello. Kawai, bisa togo da hujjar ai hukumar EFCC na bincikensa, sannan, wani shu’umin kwamiti da shugaba Obasanjo ya kafa na bincike, ya yi masa takardar alakakai “white paper”.
Ganin irin wannan kama-karya da aka yi wa Albishir, sai ya garzaya zuwa Kotu, don a dawo masa da hakkinsa na ya ci zaben cikin gida. Nan take Kotu ta goyi bayansa, tare da umartar jam’iyyar ANPP da Hukuma Zabe cewa, su mayar masa da wannan hakki nasa. Ko mai karatu kuwa ya san, jam’iyyar, ta ki mai da masa da wannan hakki nasa. Haka ita ma hukumar zabe, ta ki mayar da sunansa cikin rijista, a matsayin shi ne dan takarar kujerar gwamna karkashin inuwar jam’iyyar ANPP.
A dai wannan Shekarar zaben ta 2007, mataimakin shugaban Kasa na lokacin, Atiku Abubakar, ya soki shugabancin jam’iyyar PDP na Kasa da yi wa tsarin mulkin jam’iyya kwaskwarima, ta yadda zai rika gamsar da haramtattun muradan shugaba Obasanjo. Ta hanyar yin waccan kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin jam’iyyar ne aka rika tauye hakkin “ya”yan jam’iyyar ta PDP, musamman irin mutanen da shugaba Obasanjo ba shi son a ba su takara.
Lokacin da shugabancin jam’iyyun ke tafka irin wadancan badalolin, wa ya isa ya taka musu birki? Ba ma dan jam’iyya ba, hatta Kotuna ma an nuna musu ba su isa ba, to kuma bisa wane dalili ne idan Kotunan daga baya sun rafke kan irin wadancan “yan takara na boge, sai kuma cibi ya zama kari? Ashe, ba a na yi wa mutum gyara ne ba da irin kalar hajar da ya saya ba? Su jam’iyyun siyasun a yau, sun yarda a bar su su yi ta tafka badalarsu da sauran bidi’o’insu son ransu, amma daga bisani idan labari ya sha banban, sai su tasamma yin tsinuwa da zage-zage ga alkalai, har ma akan yi musu barazanar za a kashe su!!!. Tsakanin jam’iyyun da alkalan, waye cikinsu Allah Ya aiko, balle a ce duk abinda ya yi daidai ne? Irin wannan son zuciyar ne ya yi ajalin jam’iyyar CPC a jihar Kano a Shekarar 2011, inda Muhammad Sani Abacha ya lashe zaben cikin gida na jam’iyya, amma jagororin jam’iyyar suka bai wa Lawan Jafaru Isa takarar, a karshe aka yi cikakkiyar haihuwar guzuma…
Amfani Da Alkalai
Duk cikar jam’iyyun siyasun Nijeriya, babu daya da za a bugi kirjin ba ta yunkurin amfani da alkalai idan ta samu gaba. A wannan jamhuriyar siyasar ta hudu a nan Kano, tsakanin tsohon gwamna Kwankwaso da Shekarau da Ganduje, waye a lokacin gwamnatinsa, wata jam’iyyar adawa a Kano, ta sami nasarar lashe kujerun Ciyamomi da Kansiloli, da kashi 20 cikin 100? Zabe ne ake yinsa karkashin Hukumar Zaben da maigirma gwamna ne zai kafa shugabanta. Shi ne zai ba ta kayan aiki. Bugu da kari, idan an sami wasu korafe-korafe bayan kammala zabukan, Kotunan jihar ne ke da alhakin saurarar kararrakin, tare da yanke hukunci na karshe. A shari’un duka, ba a daukaka kara zuwa Kotun Koli. Kotunan jihar ne za su yi kidansu, su yi rawarsu.
Tambaya ga irin wadancan jam’iyyu na siyasa, da ma kai mai karatu, wane adalci ne aka samu a irin wadancan Kotuna na jihar Kano da ke yanke hukunce hukuncen zabukan majalisun kananan hukumomi a Kano, lokacin wadancan gwamnoni uku da aka lasafta a sama? Ko mai karatu na iya tuna wani hukunci da wata Kotu ta yi a jihar, game da wata kujerar karamar hukuma, inda har sai da Ciyaman din da ake karar ba shi ne halastaccen wanda ya ci zabe ba, ya kammala Shekarunsa uku cifcif bisa kujerar, sannan daga baya wai Kotu ta tabbatar ba shi ne ya lashe zaben ba. Duk rashin adalci da a yau wasu ke kallon wasu alkalai na yi wajen yanke hukuncin shari’un zabe, sai a kawo inda ga wani gwamna ko wani shugaban Kasa ya kammala zangon mulkinsa, sannan daga baya aka ce ba shi ne halastaccen wanda ya lashe zaben ba? Idan babu, ashe ma ke nan Alkalan Kotunan Shari’un Zabukan Kasa bakidaya, sun fi alkalan jihohi da gwamnoni ke da iko akansu adalci?
Lauyoyi Na Jikawa Jam’iyyun Siyasa Aiki
Mene ne amfanin lauya mai bai wa jam’iyya shawara akan lamuran shari’a? Daga cikin amfaninsa, sun hadar da dora jam’iyyar bisa doron shari’a cikin daukacin aikace aikacenta. Jan hankalin jam’iyya, don kaucewa duk wani lamari da ka iya zame mata dan-zani a Kotu. Idan an yi rashin sa’ar shigar da jam’iyyar kara Kotu, wannan lauya na jam’iyya, na iya samun kansa cikin rukunin wadanda za su tsayawa jam’iyyar a gaban mai-shari’a. Duk da irin alfanun da irin wadannan lauyoyi ke da shi ga jam’iyyun na siyasa, sai a rika ganin jam’iyyun na afkawa cikin wasu ramukan da bai kyautu su afka ba, duba da kasantuwar wadannan lauyoyi a tare da su.
Shin, lokacin gabatar da irin wadancan zabuka na cikin gida na jam’iyya, irin wadancan lauyoyi ba sa ankarar da jam’iyyun cewa, su gabatar da komai bisa doron shari’a? Ko suna nusar da su ne, amma ba a daukar shawararsu ne? Dole ne cikin dayan biyun. Ba