Wani Iftila’i ya afku a kauyen Kaura da ke Karamar Hukumar Yabo a Jihar Sakkwato, inda wasu ‘yan gida daya su bakwai suka mutu bayan sun ci abinci safe.
Magidancin da lamarin ya shafi iyalansa, Malam Danbala ya shaida wa manema labarai cewa ya rasa matansa biyu da ‘ya’yansa biyar a sanadiyyar wannan lamari.
- Yadda Bikin Cinikayyar Hidimomi Ke Jan Hankalin ‘Yan Kasuwa
- 2023: Atiku Da Tambuwal Sun Bukaci ‘Yan Nijeriya Ka Da Su Sake Zabar APC
Ya ce, “Ina Jihar Neja inda nake aiki a matsayin lebura, sai wani dan uwana ya kira ni a ranar Litinin cewa an samu matsala wadda ta bukaci kulawar gaggawa a gida.
“Ya ce in dawo gida da wuri idan zan iya. Na tambaye shi me ya faru amma sai ya katse wayar ba tare da ya yi min wani karin bayani ba.
“Saboda haka na hau motar safe zuwa Sakkwato, da na isa gida, sai na tarar da duk iyalaina, ban da wata ’yata guda duk sun mutu. An yi jana’izarsu tun kafin isowata a ranar Talata kamar yadda addininmu ya bukata.”
Danbala, ya ce matsalar ta samo asali ne lokacin da daya daga cikin matansa ta dafa Dambu domin yin karin kumallo da shi.
“Dukkansu sun ci sun koshi kuma bayan wani lokaci sai suka fara korafin ciwon ciki kuma nan take aka garzaya da su asibiti.
“Yaran biyar ne suka fara rasuwa, sai matana da suka mutu da tsakar dare amma yarinyata tana karbar magani saboda ba ta cin abinci da yawa ba,” in ji shi.
A cewar wani shaidar gani da ido, matar ta dafa abincin ne a matsayin abincin dare a ranar Lahadi.
An ce ragowar abincin an ajiye shi ne domin yin karin kumallo da shi, kuma a safiyar ranar Litinin ta hada ragowar Dambun wadda ya kwana bubude. An ce ta dafa abincin sanan ta raba wa ‘yan gidan.
“Haka ne Allah ya kaddara makomarsu. Allah ya ba su Jannatul Firdaus,” in ji magidancin da iyalansa suka rasu.