An hallaka wani dan sanda wasu kuma sun samu raunuka a lolacin da ‘yan ta’addar ISWAP suka kai harin a yankin Auno da ke a karamar hukumar Konduga cikin jihar Borno.
Auno na da tsawon kilo mita 24 da birnin Maiduguri cikin jihar Borno, ‘yan ta’addar sun kai harin ne a kan babbar hanyar Maiduguri zuwaDamaturu.
- Sin Ta Kare Matakan Martani Da Ta Dauka Kan Yankin Taiwan Saboda Ziyarar Pelosi
- Muhimmanci Koya Ma ‘Ya’ya Sana’oi Tun Suna kanana
An ruwaito cewa, ‘yan ta’addar wadanda suka fito da yawansu, sun kai wa ‘yan sandan harin ne a yayin da suke kan yin aiki a wajen duba ababen hawa.
Wata majiya ta sheda wa Zagazola Makama, wani mai fashin baki kan harkokin tsaro a tekun Chadi cewa ‘yan sanda biyu da ke kan aiki a wajen duba ababen hawa ne suka aukawa ‘yan ta’addar da harbi, inda hakan ya janyo mutuwar ‘yan sandan.
Ya ce, jin harbe-harben ya sa sauran ‘yan sanda suka kawo dauki zuwa gurin suka kuma fafata Da ‘yan ta’addar , inda hakan ya sa ‘yan ta’addar suka ja da baya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp