Wani yaro dan shekara 14, Ashfa Ibrahim, ya nutse a wani rafi a kauyen Danzaki da ke karamar hukumar Gezawa a Jihar Kano ranar Litinin.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin Hukumar Kashe Gobara ta jihar, Alhaji Saminu Abdullahi, kuma ya bayyanawa manema labarai a Kano ranar Talata.
- 2023: Duka Ma’aikatan Wucin Gadi Sai Sun Yi Rantsuwar Yin Adalci Ga Kowacce Jam’iyya – INEC
- 2023: Jerin Ayyukan Ma’aikatan Zabe Na Dindindin Da Na Wucin Gadi
Sanarwar ta nuna cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin.
“Mun samu kiran gaggawa daga wani Ibrahim Abdullahi kuma mun aika tawagarmu zuwa wurin amma an ceto wanda abin ya shafa daga rafi a sume,” in ji shi.
“Daga likitocin Babban Asibitin Gezawa suka tabbatar da mutuwar wanda abun ya shafa,” in ji shi.
A cewarsa, wanda abin ya shafa ya zame ya fada cikin ruwan, inda ya samu raunuka a jikinsa.
Ya ce tuni aka mika gawar ga Hakimin Kauyen Danzaki, Muhammed Abdulkarim, domin kaita ga iyayensa don yi masa jana’iza.
Hukumar Kashe Gobarar ta mika lamarin zuwa ga ‘yansanda domin gudanar da bincike tar da gano musabbabin faruwar lamarin domin daukar matakin da ya dace.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp