Dan takarar jam’iyyar NNPP, Barista M.B Shehu an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben dan majalisa mai wakiltar Fagge a Jihar Kano.
Shehu ya kayar da dan majalisar wakilai mai ci mai wakiltar Fagge, Aminu Sulaiman Goro na jam’iyyar APC, wanda ke wa’adi na uku a majalisar wakilai.
- Kin Amincewa Da Kwangilar Dala Miliyan 22 Ta Yi Sanadiyyar Sauke Ni Daga Shugabancin NPA –Hajiya Hadiza Bala-Usman
- Me Ya Sa ‘Yan Kasuwar Kasashen Waje Ke Da Kwarin Gwiwa Game Da Kasar Sin? Baje kolin Kayayyakin Masarufi Ya Ba Da Amsa…
Da yake bayyana sakamakon zaben bayan kammala zaben na ranar Asabar, jami’in zaben Farfesa Ibrahim Tajo Suraj, ya ce Shehu ya samu kuri’u 19,024 daga cikin kuri’un da aka kada, sai dan takarar jam’iyyar Labour, Shu’aibu Abubakar, wanda ya samu kuri’u 12,789.
Sakamakon zaben dai Aminu Sulaiman Goro na jam’iyyar APC ya zo na uku da kuri’u 8,669.
“MB Shehu na jam’iyyar NNPP, bayan ya cika sharuddan doka kuma ya samu mafi yawan kuri’u an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben,” in ji jami’in zaben.
Tun da farko dai, jam’iyyar NNPP ce ke kan gaba da kuri’u 609 a zaben ‘yan majalisar da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, yayin da APC ta zo ta biyu da kuri’u 268, sai LP da kuri’u 60.
Sai dai a lokacin da aka kammala hada sakamakon zaben bayan kammala zaben na ranar 14 ga watan Afrilu, jam’iyyar NNPP ta lashe zaben.