Shahararren dan wasan kwallon kafa na gaba a Kungiyar Dortmund dake gasar kofin Bundes liga ta Kasar Jamus, Erling Haaland ya Kammala komawa Sabuwar Kungiyarsa ta Ingila, Manchester city.
Haaland ya yaba wa mahaifinsa Alf-Inge don sa masa soyayyar Sabuwar kungiyar ta Manchester City.
Alf-Inge mahaifin Erling Haaland ya koma Ingila ne a shekarar 1993 daga bisani ya zama Dan kwallon Kungiyar Manchester City a shekarar 2000, inda ya buga wa kungiyar wasa sau 45, kafin ya samu rauni a gwiwarsa, sakamakon karon batta da yayi da dan wasan kungiyar Man United, Roy Keane ayayin wani wasan kiyayye(derby), wanda hakan ya tilasta masa yin ritaya da wuri a 2003.
Matashin Haaland, wanda aka haife shi a Leeds, kasar Ingila a shekarar 2000, yanzu ya yarda da bin sahun mahaifinshi, Alf-Inge bayan yanke shawarar shiga kungiyar Man City yana dan Shekara 22.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp