Wani faifan bidiyo da ya yadu a shafin sada zumunta ya nuna wani limamin Catholic yana gaya wa ‘yan cocinsa da ba su da katin zabe na dindindin (PVC) su koma gida.
Masu amfani da shafin na Twitter da dama ne suka yada bidiyon, ciki har da wani mai fafutukar siyasa, Rinu Oduala, wanda ya kasance kan gaba wajen fadakarwa akan yin katin zaben (PVC).
Duk da cewa har yanzu babu cikakken bayani kan inda lamarin ya faru da kuma lokacin da lamarin ya faru, amma malamin kamar yadda aka gani a faifan bidiyon ya jaddada cewa “Ba sai kazo Cocinsa ba in har baka da katin dindindin na zabe a hannunka.”
Jaridar Vanguard ta kara da cewa: taji Malamin Yana cewa “Kuzo mu taru a wajen ibada in kuna da katin zabe (PVC), in baku da shi, ba sai kunzo ba.
“Saboda babu wata fa’ida a ce kiristoci sun cika coci, amma a lokacin zabe, kadan ne daga cikinsu zasu fito domin kada kuri’a.”
Don haka, Malamin Yana nufin ya Kamata Kiristoci su dauki alhakin zabe da Muhimmanci.