Dangantakar kasuwanci tsakanin Nijeriya da kasar Sin ta kara karfi, bayan kaddamar da zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci da kamfanin jiragen sama na Air Peace, ya yi zuwa birnin Guangzhou na kasar Sin.
A ranar Laraba ne kamfanin Air Peace ya fadada jigila zuwa Asiya tare da fara zirga-zirgar jiragen sama kai tsaye na mako guda zuwa kasar Sin.
- Kiristoci Kada Su Damu Da Takarar Musulmi 2 – Shugaban Jam’iyyar APC
- Mata 700,000 Ke Mutuwa Duk Shekara Sanadin Dajin Mama
Jirgin da ya tashi da misalin karfe 22:00 na da jimillar fasinjoji 240 wadanda aka yi ta daga sabuwar tashar da aka kaddamar kai tsaye zuwa kasar Sin ta jirginsa Boeing 777.
Kazalika, kamfanin ya bayyana cewa, ana shirin hada biranen Beijing, da Shanghai da sauran biranen Nijeriya, ta hanyar yin amfani da tsarin layin dogo da wani kamfanin jiragen sama na Asiya.
Da take jawabi yayin kaddamar da jirgin, babbar jami’ar gudanarwa na kamfanin Air Peace, Oluwatoyin Olajide, ta bayyana cewa, kamfanin ya yi hasashen kamfanin zai samar da dimbin ayyukan yi ga ‘yan Nijeriya da kuma rage wa ‘yan Nijeriya nauyin tafiye-tafiyen jiragen sama, da kuma sauran ‘yan Afirka ta hanyar samar da ayyukan yi na hadin kai mai araha da lumana a cikin birane da nahiyoyi.
Ta ce: “Yanzu, za mu iya tabbatar da cewa Air Peace ya yi wannan hangen nesa don fadada hanyar sadarwar da ake da su don biyan bukatun tafiye-tafiye a sama na jama’a masu. A yau, muna kara kaimi zuwa nahiyar Asiya a hukumance, tare da fara jigilar jirgin farko na mako guda zuwa Guangzhou-Si .
“Idan har kuna bibiyar ci gaban da kamfani na Air Peace ke yi, za ku san cewa sararin samaniyar kasar Sin ba sabon abu ba ne a gare mu, domin mun samu nasarar gudanar da jigilar jiragen sama na musamman zuwa kasar a lokuta daban-daban a baya, musamman a 2020, lokacin kullen Korona.
“Don haka, za mu shiga kasar Sin, ba a matsayin sababbi ba, amma a matsayin kamfanin jirgin sama wanda ya kware a fannin fasaha da aiki tare da kasar Sin. Jama’a masu tashi, musamman ma wadanda ke tashi daga hanyar Guangzhou, ya kamata su yi tsammanin kwarewar jirgin sama mafi inganci, wanda ke da alama ta Air Peace.
“Ba mu tsaya a iya Guangzhou ba – Indiya ce ta gaba kuma Isra’ila ma na cikin tsarinmu. Haka kuma ana shirin kaddamar da aikinmu a Malabo a Equatorial Guinea da Kinshasa a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.
“Za mu ci gaba da habaka hanyoyin sadarwarmu tare da sabunta dabaru. Air Peace a halin yanzu yana alfahari da hanyar sadarwa na hanyoyin cikin gida guda ashirin, hanyoyin yanki guda bakwai da wurare biyu na duniya, ciki har da Dubai da Johannesburg.”
Olajide, wadda ta amince da rawar da hukumomin gwamnati da ma’aikatar sufurin jiragen sama suka taka wajen cimma nasarar, ta ce adadin jigilar zai karu da zarar hukumomin kasar Sin sun sassauta dokokin Korona.
A cewarta, jirgin zai kara dankon zumunci tsakanin Nijeriya da Sin duk da cewar kasashen biyu za su ci gajiya sosai daga ayyukansu na jiragen kai tsaye.
Ta ce, “yau za mu fara jigilar jirgin mu na farko kai tsaye zuwa kasar Sin, idan muka yi la’akari da yawan al’ummar Sinawa a Nijeriya da aikin da suke yi wa Nijeriya, za mu iya tunanin irin tasirin da ya yi kan tattalin arziki. Don haka, idan za mu yi jigilar kai tsaye tsakanin Nijeriya zuwa kasar Sin, hakan zai karfafa dankon zumuncin da ke tsakanin kasashen biyu, zai kuma kara samun kudaden shiga da ake samu daga cudanya da tattalin arzikin kasashen biyu.
“Wannan dangantaka ce da Air Peace ta samu damar samarwa sannan kuma muna fatan ta zama babbar fa’ida.
Ta kara da cewa, “Yayin da muke fara jigilar Guangzhou a yau, dole ne mu yaba wa hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Nijeriya, NCAA, hukumar kula da filayen jiragen sama ta Nijeriya, FAAN, ma’aikatar sufurin jiragen sama, gwamnatin kasar Sin, abokan huldarmu, da sauran masu ruwa da tsaki kan tabbatuwar hakan. Mun yi alkawarin yin aiki cikin jituwa tare da kowa don tabbatar da cewa an inganta wannan sabuwar tafiya. ”