Kamfanin Dangote ya musanta labarin da ya karade kakafen yada labarin da ke nuni da cewa kamfanin mai na kasa ya kinkimo bashin dala biliyan guda domin tallafa wa matatan man Dangote.
Dangote ya musanta labarin ne cikin wata sanarwa wanda mai magana da yawun kamfanin, Anthony Chiejina ya fitar a ranar Laraba.
- Shugaba Xi Jinping Ya Isa Yankin Macao
- Tinubu Ya Isa Legas Don Gudanar Da Bukukuwan Kirsimeti Da Sabuwar Shekara
Sanarwar ta ce, “Mun samu tambayoyi da dama daga kafafen yada labarai da sauran masu ruwa da tsaki da ke neman qarin haske kan wani rahoto na baya-bayan nan da aka danganta ga kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPCL), cewa matakin da suka dauka na samun lamuni na dala biliyan 1 daga danyen mai na tallafa wa matatar ta Dangote a lokacin da ya fuskanci kalubalen ba gaskiya ba ne.
“Muna so mu fayyace cewa wannan kuskure ne na lamari, domin dala biliyan 1 kusan kashi 5 ne na jarin aka kashe wajen gina matatar Dangote.
“Shawarar da muka yanke na kulla kawance da NNPCL ya ta’allaka ne kan amincewa da dabarunsu a masana’antar a matsayinsu na masu safarar danyen man fetur mafi girma a Nijeriya a wannan lokacin, su ne kadai suke samar da man fetur a Nijeriya.
“Mun amince kan sayar da hannun jarin kashi 20, kan darajar dala biliyan 2.76. Daga cikin wannan, mun amince da cewa za su biya dala biliyan 1 ne kawai yayin da za a kwato ma’auni na tsawon shekaru 5 ta hanyar cire mana danyen mai da suke kawo mana da kuma ribar da ake samu. Idan da muna cikin kalubalen kudi da ba mu ba su irin wadannan sharuddan biyan kudi masu yawa ba. Kamar yadda a 2021, lokacin da aka sanya hannu kan yarjejeniyar, matatar ta kasance a matakin farko. Bugu da kari, da a ce muna da matsalar kudi, da wannan yarjejeniya ta kasance an biya tsabar kudin nan take.
“Sai dai kuma abin takaicin shi ne, daga baya kamfanin na NNPC ya kasa samar da ganga dubu 300 da aka amince da shi a rana na danyen mai ganin cewa sun sadaukar da mafi yawa daga cikin danyen da suka samu ga masu kudi tare da fatan samun karin hako mai wanda suka kasa cimma ruwa.
“Daga nan kuma muka ba su wa’adin watanni 12 domin su biya cikon kudadensu ganin yadda suka kasa samar da adadin danyen mai da aka amince da su. Kamfanin NNPCL ya gaza cika wannan wa’adin da ya kare a ranar 30 ga watan Yunin 2024. Sakamakon haka, an sake bitar kason su zuwa kashi 7.24. Dukkan bangarorin biyu sun ba da rahoton wadannan abubuwan da suka faru.
“Don haka, ba daidai ba ne a yi ikirarin cewa NNPCL ya ciyo bashin dala biliyan 1 domin tallafa wa matatar man Dangote. Kamar duk abokan huldar kasuwanci, NNPCL ya zuba jarin dala biliyan 1 a matatar man domin samun hannun jarin na kashi 7.24 wanda zai amfanar da muradunta,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta qara da cewa Kamfanin NNPCPL ya kasance abokin hulda mai kima wajen samun ci gaba, kuma ya zama wajibi ga duk masu ruwa da tsaki su kiyaye gaskiya tare da gabatar da sahihin labari, don jagorantar kafafen yada labarai wajen bayar da sahihin rahoto wanda zai amfanin masu ruwa da tsaki da daukaci al’umma.