• English
  • Business News
Saturday, October 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dangote Ya Sake Zama Wanda Ya Fi Kowa Kudi A Afrika Karo Na 12

by Sadiq
2 years ago
Dangote

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Aliko Dangote ya zama attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka karo na 12 a jere, kamar yadda mujallar Forbes ta ruwaito.

Babban kamfanin Dangote na siminti ne ya ci gaba kasancewa kan gaba wajen samar da siminti a Afirka, kuma Dangote shi ne dan Nijeriya daya tilo a cikin jerin attajirai 200 na farko a duniya wanda darajarsa tai kai dalar Amurka biliyan 14.2, sama da dala biliyan 12.1 da ya samu a bara.

  • Gwamnatin Kano Za Ta Dauki Nauyin Karatun Dalibai 1,100
  • Tinubu Ya Bada Umarnin Binciko Wadanda Suke Kashe-Kashe A Filato

A halin yanzu Dangote yana matsayi na 124 a cikin manyan attajiran duniya, kuma shi ne dan Nijeriya daya tilo a cikin jerin manyan attajiran duniya 200 kuma daya daga cikin ‘yan Afirka biyu da ke jerin attajirai; tare da Johann Rupert na Afirka ta Kudu, wanda ya zo na 157 da darajar dukiyar da ta kai dala biliyan 11.1.

Attajirin wanda ya fi kowa kudi a Afirka na jagorantar kamfanin siminti mafi girma a nahiyar Afrika.

Kamfanin siminti na Dangote na samar da tan miliyan 51.6 a kowace shekara a kasashe goma a Afrika, tare da hadakar masana’antu a kasashe bakwai da kuma wasu masana’antu a Kamaru da Ghana da Saliyo.

LABARAI MASU NASABA

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

Gwarzon Ma’aikacin Lafiya Na Shekarar 2025 Dakta Seidu Adebayo Bello

Dangote ya mallaki kamfanonin gishiri da sukari da ma wasu daban.

Kazalika, attajirin ya mallaki matatar tace mai, wadda ake kyautata zaton za ta zama mafi girma a duniya, wadda tsohon shugaban kasar Nijeriya, shugaba Buhari ya kaddamar kuma ana sa ran za ta sarrafa gangar mai 650,000 don amfanin cikin gida da kuma fitar da shi zuwa kasashen waje.

Mujallar Fortune, wata mujalla ce ta kasuwanci ta kasa da kasa da ke Amurka, ta ayyana Dangote a matsayi na 11 cikin mutum 50 mafi tasiri a duniya a tsakanin ‘yan kasuwa maza da mata.

Mujallar da aka fara buga ta a watan Fabrairun 1930, ta ce attajirim na sauya duniya tare da zaburar da wasu a harkokin kasuwanci da gwamnati wajen ciyar da al’ummarsu gaba.

Dangote ya samu matakin ne bayan da mujallar ta ce attajirin yana amfani da dukiyarsa ta hanyar taimakon jama’a ta gidauniyarsa ta Aliko Dangote.

Mutum 10 maza da mata da mujallar Fortune ta zayyano a matsayin wadanda suka fi kowa tasiri su ne: Bill da Melinda Gates, Jacinda Ardem, Robert Mueller, Pony Ma, Satya Nadella, Greta Thunberg, Margrethe Vestager, Anna Nimiriano, Jose Andres, da Dough Mcmillon da Lisa Woods.

Shi kuwa Dangote an ayyana shi a matsayin daya daga cikin manyan ‘yan kasuwa a fadin duniya wanda ya cancanci a karrama shi ta hanyar basirar kasuwancinsa da kuma ayyukan alheri.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu
Manyan Labarai

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji
Manyan Labarai

Gwarzon Ma’aikacin Lafiya Na Shekarar 2025 Dakta Seidu Adebayo Bello

October 25, 2025
Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria
Tattalin Arziki

Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria

October 25, 2025
Next Post
Mark Zuckerberg Ya Fara Daukar Horo Don Yin Dambe Da Elon Musk

Mark Zuckerberg Ya Fara Daukar Horo Don Yin Dambe Da Elon Musk

LABARAI MASU NASABA

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

October 25, 2025
An Kaddamar Da Nuna Muhimman Shirye-shiryen CMG A Membobin APEC

An Kaddamar Da Nuna Muhimman Shirye-shiryen CMG A Membobin APEC

October 25, 2025
Zuwan Tsoffin ’Yan Wasan Barcelona Abuja Ya Nuna Ana Samun Zaman Lafiya A Nijeriya – Matawalle

Zuwan Tsoffin ’Yan Wasan Barcelona Abuja Ya Nuna Ana Samun Zaman Lafiya A Nijeriya – Matawalle

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Lafiya Na Shekarar 2025 Dakta Seidu Adebayo Bello

October 25, 2025
Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria

Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria

October 25, 2025

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kaya Na Shekarar 2025, Kamfanin Nestlé Pure Life

October 25, 2025
Mata Ne Ginshikin Ci-Gaban Al’umma – Gimbiyar Dange

Mata Ne Ginshikin Ci-Gaban Al’umma – Gimbiyar Dange

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Mawaƙin Shekarar 2025, Skales

October 25, 2025
Jami’ar ABU Ta Ƙaryata Zargin Ƙera Makamin Nukiliya A Asirce

Jami’ar ABU Ta Ƙaryata Zargin Ƙera Makamin Nukiliya A Asirce

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Hukumar Kare Ƴancin Masu Amfani Da Kaya (FCCPC): Tabbatar Da Adalci A Kasuwa

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.