• English
  • Business News
Monday, October 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dantsoho Ya Kaddamar Da Aikin Tsaftace Tashar Jirgi Ta Tin-Can Island

by Bello Hamza
5 months ago
Dantsoho

Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, tare da hadaka da Gwamnatin Jihar Legas da sauran wasu masu ruwa da tsaki a bangaren tsaro, domin fadar kan jama’a kan mahimmancin tsaftace Tashar Jirgi ta Tin Can Island, da ke a jihar.

Hakan na kunshe ne, a cikin sanarwar da Hukumar ta fitar, inda sanarwar ta bayyana cewa, za ta yi hakan ne, bisa nufin magance duk wasu ayyuka da ke janyo tarnaki a Tashar ta Tin Can Island, musamman domin a samar da walwalar gudanar da ayyuka a Tashar, a cikin sauki.

  • Darajar Cinikayyar Waje Ta Sin Ta Karu Da Kaso Shida Bisa Dari A Afirilu
  • Tsaro Ya Inganta A Zamfara, In Ji Gwamna Lawal Yayin Tattakin Zaman Lafiya Na Tarihi A Jihar

Kazalika, sanarwa ta bayyna cewa, manufar shi ne, domin a dakile ayyukan batagari da sauran masu kaffa shugana a Tashar, ba bisa ka’ida ba, wanda hakan, ke haifar da cunkoson ababen hawa, a Tashar, inda hakan ya zama barazana da lafiyar ma’aikatan da ke a Tashar ta Tin Can Island.

Aikin na tsaftace Tashar Jirgi ta Tin Can Island, ya yi daidai da tsarin kasa da kasa, musamman wajen kara tabbatar da tsaro da wanzar da matakan kungiyar IMO da ke tabbatar da kare zirga-zirgar Jiragen Ruwa a Tekuna, na kasa da kasa, musamman domin a kara tabbatar da samar da kariya da kuma tsaro, adaukacin Tashoshin Jiragen Ruwa, a fadin duniya.

Da yake kaddamar da aikin tsaftace Tashar Jirgen Ruwan ta Tin Can Island, Shugaban Hukumar ta NPA Abubakar Dantsoho ya bayyana cewa, Hukumar ta dauki wannan matakin ne, domin ta tabbatar da samar da kyakyawan yanayi wanda ya yi daidai da na kasa da kasa da kuma kara bunkasa tattalin arzikin kasar nan.

LABARAI MASU NASABA

Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kaya Na Shekarar 2025, Kamfanin Nestlé Pure Life

“Ya zamar mana wajbi, mu kulla wannan hadakar, musamman domoin mu tabbatar da cewa, mun tsaftace tsarin,” Inji Dantsoho.

Ya kara da cewa, wannan aikin, ba wai kawai za kara habaka samar da kariya da kuma kara ingnata tsaro bane, har da kuma bayar da gagarumar gudunmawa, wajen kara ciyar da tattalin arzikin kasar nan gaba.

A cewar Shugaban, cunkoson da ake samu a Tashar ta Tin Can Island na ci gaba da haifar da jinkiri da rashin gudanar da ayyuka yadda suka kamata da kuma rage gudanar da hada-hadar kasuwanci, yadda ta kamata, wanda kuma hakan, ke janyowa kara habaka tattalin arzikin kasar.

Dantsoho wanda Babban Janar Manaja na sashen kula da tsaro a Hukumar ta NPA Mista Anthony Edosomwan ya wakilce shi a wajen kaddamar da aikin ya bayyana cewa, za a gudanar da aikin ne, zuwa kwana uku, musamman domin a samu nasarar gudanar da aikin.

Shugaban ya kara da cewa, sashen kula da tsaro na Hukumar ya wallafa a kafafen yada labarai, kan sanarwar wayar da kan jama’a kan batun mahimmancin, tsaftace Tashar ta Tin Can Island.

“Wannan wani mataki ne, da aka samu goyon bayan masu ruwa da tsaki ciki har da masu yin amfani da Tashar da ‘yan kasuwa da kuma sauran alummar da ke a kusa da yankin”, A cewar Dantsoho.

Shugaban ya ci gaba da cewa, Hukumar ta NPA ba za ta yi kasa a guiwa, wajen kara mayar da hankali da kuma zagewa, domin ta samu cin nasara wajen tabbatar da tsaftace muhalli da kuma samar da kyakyawan yanayi, a daukacin Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar ba.

“Yanayi na samun gurbatacciyar Iska da kutsen da ake yiwa Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar, abu ne da Hukumar ta NPA, ba za ta rungume hannu ta bari ba, ” Inji Dantsoho.

“Wannan aikin na tsafrace Tashar ba wai kawai na da alfanu ga ayyukan da ake gudanarwa a Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar bane, hatta alumomin da suke daura da Tashoshin, suma zai yi masu alfanu,“ A cewar Shuaban .

Shuaban ya kara da cewa, sashen kula da tsaro na Hukumar ta NPA da faro shi a wannan shekarar ta 2025, na daga cikin shiryae-shiryen rage cunkoso da kuma samar da saukin gudanar da ayyuka, Hukumar ta NPA, wanda hakan zai taimaka matuka wajen samar da kyakywar makoma ga Tashoshin Jiragen Ruwa, da ke a daukacin kasar nan.

A cewar Shugaban, wannan hadakar da sauran jami’an tsaro da kuma yin gangamin na wayar da kan alumma, Hukumar na bukatar goyon bayan alumma, dominn ta samu nasarar, aikin da ta sanya a gaba,

“A saboda haka, Mahukuntan Hukumar ta NPA, na bukatar goyon baya da hadin kan jama’a musamman domin a samar da kyakyawan yanin da ya dace a Tashar Jirgin Ruwan,” A cewar Shugaban.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria
Tattalin Arziki

Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria

October 25, 2025
Tattalin Arziki

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kaya Na Shekarar 2025, Kamfanin Nestlé Pure Life

October 25, 2025
Tinubu Ya Amince A Fara Aikin Tashoshin Jiragen Ruwa Na Apapa Da Kalaba Da Fatakwal Da Warri — NPA
Tattalin Arziki

Tinubu Ya Amince A Fara Aikin Tashoshin Jiragen Ruwa Na Apapa Da Kalaba Da Fatakwal Da Warri — NPA

October 17, 2025
Next Post
Rashin Daukar Tsauraran Matakai Na Iya Durkusar Da Bangaren Noma – Shehu Galadima

Nau’ikan Amfanin Gona Da Ke Saurin Girma Cikin ‘Yan Watanni

LABARAI MASU NASABA

An Zaɓi Birgediya Janar Yake A Matsayin Sarkin Sayawa Na Farko Duk Da Zanga-zanga 

An Zaɓi Birgediya Janar Yake A Matsayin Sarkin Sayawa Na Farko Duk Da Zanga-zanga 

October 27, 2025
Dantsoho

Tsohon Gwamnan Jigawa, Lamido Ya Bayyana Aniyar Takarar Shugabancin Jam’iyyar PDP Na Ƙasa

October 27, 2025
Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

October 27, 2025
Hatsarin Jiragen Ruwa

Matasa 5 Sun Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Gombe

October 27, 2025
Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025
Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

October 26, 2025
“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

October 26, 2025
Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

October 26, 2025
Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

October 26, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.