A ranar Laraba 25 ga watan Mayu 2022 ne, Dakta Dauda Lawal ya samu nasarar zama dan takarar Gwamna na jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara a zaben da za a gabatar a 2023.
Babban abu mafi muhimmanci a siyasa shi ne samar da shugabanin masu nagarta da aminci.
Haka kuma babban makasudin gudanar da zaben fidda gwani a jam’iyyu shi ne samar da damar zabar wadanda al’umma suke so, suka kuma tabbatar da za su yi musu aiki yadda ya kamata, kuma wanda al’umma ke matukar kauna. A kan haka dole a jinjina wa shugabanni da ‘yan jam’iyyar PDP reshen Jihar Zamfara bisa yadda suka gudanar zaben fidda gwani a cikin nasara, inda suka zabo Dakta Dauda Lawal a mastayin wanda zai fafata da sauran jam’iyyu don neman kujerar gwamnan Jihar Zamfara.
Mulkin Jiha kamar Zamfara mai cike da kalubale daban-daban kuma a irin wannan lokaci na mulki dimokradiyya abu ne mai matukar wahala, amma yayin da aka samu kwarewa da sanin makaman aiki abin zai zama da matukar sauki.
A karon farko a tarihin Jihar Zamfara za a tafka zaben Gwamna da kwareraren dan takara Dakta Dauda Lawal. Ga jerin wasu abubuwa masu muhimmanci guda 12 da ya kamata ka sani dangene da Dakta Dauda Lawal:
1. An haife shi a ranar 2 ga watan Satumbar 1965 a garin Gusau, babban birnin Jihar Zamfara. Ya yi digirinsa na farko a fannin Kimiyyar Siyasa (Political Science) a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya dake Jihar Kaduna. A bisa yaba wa a kan harkokinsa na tallafa wa al’umma ne ya sa Jami’ar Usman Danfodio Sakkwato ta karrama shi da digirn-digirgir, Haka kuma Jami’ar IHERIS ta kasar Togo ita ma ta karrama shi da digirin-digirgir, yana kuma daga cikin wadanda aka karramar a babban taron ‘African Achiebers Award 2021’ da aka yi a Kensington Palace da ke Landan a kasar Birtaniya.
2. Bayan dawowarsa gida Nijeriya a shekarar 2003, Dauda Lawal ya shiga aikin Banki da ayyukan tallafa wa al’umma, ya kuma samu halartar kwasa-kwasai da dama a ciki da wajen Nijeriya; ciki har da Babbar Makarantar Kasuwanci ta ‘Harbard Business School’ da ke Amurka, Makaratar Kasuwanci ta ‘London Business School’, da ‘Wharton Business School’ da ke Pennsylbania, da ‘Odford Unibersity Business School, International Faculty of Finance, da ke Landan, da ‘Fitch Training’ da ke Landan da New York, haka kuma ya halarci ‘The Asian Banker, Accenture’ da ‘Lagos Business School’, da kuma ‘Euromoney, Ernst and Young’ a inda ya sami cikakkiyar kwarewa a fanin sarrafawa da mu’amala da kudi a mahangar masanan bangaren duniya.
3. Dakta Dauda Lawal ya yi aiki tukuru don ya cimma burinsa. Ya yi aiki a kwamitin gudanarwa First Bank a shekarar 2012 daga nan ne aka dauke shi aiki a matsayin Babban Darakta mai kula yankin Arewa. Ya kuma zama mataimakin shugaba mai kuma da bangaren kamfanoni masu zaman kansu na yankin arewa, ya kuma rike manyan mukamai a bankin ciki har da Babban Manaja mai kula da harkokin kasuwanci (BDM) a reshen bankin na unguwar Maitama dake Abuja, inda ya samu nasarar bunkasa harkokin bankin a babban birnin tarayya da kewaye.
4. Yana da sanin makaman aiki na fiye da shekara 26 wanda ya hada da kwarewa a bangaren kasuwanci da bangaren kamfanoni masu zaman kansu. Tsayuwa da kwarewarsa ta kashi ga matsayinsa na yanzu na Babban Darakta. Sau biyu yana karbar lambar karramawa a matsayin gwarzon shugaban bankin ‘First Bank’, a shekarar 2006 ya zama “Gwarzon Manaja Mai Bunkasa Kasuwanci”, a shekarar 2009 kuma ya samu kyautar “Gwarzon Ma’aikaci Mai Kawo Cigaba”.
5. Dakta Dauda Lawal mamba ne a kungiyoyin masana da dama da suka hada da ‘Institute of Credit Administration of Nigeria’, ‘Fellow of the Cibilian Institute of Democratic Administration of Ghana’, ‘Member of the Institute of Directors, Nigeria’, African Business Roundtable’ da kuma ‘Institute of Corporate Administration, Nigeria’.
6. Dakta Dauda Lawal ya yi fiye da shekara 25 yana aiki a bangaren Bankuna, ya fara tun daga kasa har zuwa kololuwar mataki a aikin bankin. A shekarar 2018 ya ajiye aiki a matsayin Babban Darakta a ‘First Bank’, banki mafi dadewa a Nijeriya. Lawal na kashe kudadensa ne don tallafa wa al’umma musamman a bunkasa ilimi.
7. Ana iya ganin irin tallafin da Lawal yake yi musamman a Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Gusau inda ya gina hanya mai tsawon kilomita uku da rabi, da dakin maigadi a babar kofar shiga jami’ar. Ya kuma gina dakin dalibai mata guda 350 na dalibai maza guda 250 a makarantar Jinya da Unguwar Zoma ta Gusau, ya kuma biya kudaden da aka tantance kwasakwasan da ake karantarwa a makarantar. Ya kuma samu nasarar gina dakin karatu guda hudu a makarantar Kiwon lafiya ta Tsafe. Ya gina masallatai da islamiyyu da dama ya kuma gina makarbar na zamani a garin Gusau.
8. Tallafin da Lawal yake bayarwa ya wuce jiharsa ta Zamfara, ya gina azuzuwa a makarantar ‘Yan sanda ta Kaduna; ya kuma gina Masallaci da islamiyya dukkaninsu a Kaduna. Ya gyara azuzuwa da dakin daukar darasin kwamfuta a Makarantar Sakandire ta Gwamnati da ke Kachia a Jihar Kaduna. Haka kuma shi ne ya gida babban masallacin Juma’a na ITN a Zariya, ya kuma gyara shaharariiyar masallacin nan na tashar jirgin kasa da ke Kaduna.
9. A Jami’an Ahmadu Bello Zariya, inda ya yi karatun jami’arsa, ya gina dakin karatu mai hawa uku hade da ofishoshin ma’aikata, ya kuma samarwa tsangayar kimiyyar siyasa mota bas don zirga zirga. Ya kuma gina rukunin azuzuwa a tsangayar koyar da kiwon lafiya ta Jami’ar Usman Danfodio da ke Sakkwato.
10. Haka kuma Dauda Lawal ya kai tallafi kauyen Guga ta Jihar Katsina, mahaifar mahaifiyarsa inda a nan ne ya yi makarantar firamarensa, ya gina asibiti na zamani, ya gyara makarantun garin, ya samar da cibiyar koyar da kwanfuta, ya kuma samar musu da rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana (solar).
11. Don rage zaman kashe wando da samar da ayyukan yi ga al’umma Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya samar da ma’aikatar yin blok na ‘Zam blocks’, gidan blok mafi girma a Jihar Zamfara. Ya kuma kafa kamfanin shinkafa ta ‘Zam rice mills’ da kamfanin ruwa na ‘Azuma water’ da kamfanin takin zamani na ‘Zam agrochemical’ (Kamfanin taki mafi girma a arewacin Nijeriya).
12. a ranar 30 ga watan Janairu 2022, dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya dauki nauyin ‘yan asali Jihar Zamfara 120 zuwa Jami’ar IHERIS ta kasar Togo don don suyi karatu a matakin digirin farko dana biyu. Tallafin karatun ga dalibai 120 an yi ne ta hannun gidauniyar Dr. Dauda Lawal, za kuma su yi karatu ne a bangarorin Ilimin Kwamfuta, Kimiyya da Fasaha, Ilimin tafiyar da harkokin gwamnati, Harkokin kasashe waje, Ilimin sarrafa kwanfuta da sauransu.
Tabbas Jihar Zamfara ta yi dace da samun haziki kuma kwararre irin Dauda Lawal, muna fatan al’umma za su bashi goyon baya don kai Jihar Zamfara tudun-mun-tsira.