Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa gwamnonin Nijeriya baki dayansu za su hada kai ba tare da nuna bambancin jam’iyya ko siyasa ba, domin share wa Kungiyar Kwadugo (NLC), hawayen kan koke da ta kawo na rashin bude jami’o’in Nijeriya sakamakon yajin aiki da Kungiyar Malaman Jami’o’in Nijeriya (ASUU) take yi kimanin wata biyar da suka gabata.
Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne a ranar Talata a lokacin da Kungiyar NLC reshen Jihar Kano karkashin shugabancin Kwamarade Kabiru Ado Munjibiri ta zo gidan don mika kokanta ga Gwamnan Kano zuwa ga Gwamnatin Tarayya, wanda gwamnan ya tarbi ayarin kungiyar NLC da ta jagoranci gammayar kungiyoyin ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni da sauran kungiyoyin sa-kai na farar hula da nufin tillasta wa gwamnatin tarayya kan sasantawa da kungiyar ASUU domin bude jami’o.
’in ta yadda dalibai za su ci gaba da karatu. Zanga-zangar mai taken ”Yaranmu su koma makaranta.”
Har ila yau, Gwamna Ganduje ya bayyana cewa matsayin ilimi babba ne don haka rashin yin karatu a jami’o’in Nijeriya matsala ce gagaruma wanda dole su tashi tsaye wajen kawo karshen yajin aikin ASUU.
Shi ma a nasa jawabin shugaban NLC reshen Jihar Kano, Kwamarde Kabiru Ado Munjibir, wanda ya jagoranci zanga-zangar ya yaba wa Gwamnan Kano, Dakta Ganduje kan yadda yake biyan malaman jami’o’i mallakar Jihar Kano albashi duk da yajin aiki sabanin gwamnatin tarayya.
Kwamarde Munjibir ya ce wannan tattaki na zuwa gidan Gwamnatin Kano amsa umarni ne na NLC ta kasa, domin mika kuka da yadda daliban suke zaune a gida sakamakon rufe jami’o’in kasar nan.