• English
  • Business News
Friday, September 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Daular Sakkwato Ta Buga Littattafan Malaman Musulunci Miliyan 3.2 —Sarkin Musulmi

by Leadership Hausa
2 years ago
in Manyan Labarai
0
Daular Sakkwato Ta Buga Littattafan Malaman Musulunci Miliyan 3.2 —Sarkin Musulmi
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar II, ya bayyana cewa akalla litattafai miliyan 3.2 daga ayyukan Malaman Addinin Musulunci 200 na Daular Usmaniyya ne aka gyara tare da buga su don rarraba su a fadin kasar nan.

Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen wani taro na kwanaki uku kan koyar da Addinin Musulunci a Afirka wanda ya gudana a dakin taro na Arewa House da ke Jihar Kaduna a ranar Talata.

  • An Daure Wata Mata Kan Yi Wa Yaro Dan Shekara 8 Fyade
  • Matar Aure Ta Watsa Wa Budurwar Mijinta Ruwan Zafi A Fuska A Bauchi

Taron ya samu hadin gwiwar kungiyar hadin kan kasashen musulmi (OIC) da cibiyar bincike kan al’adun Musulunci da tarihin Musulunci (IRCICA) Turkiyya da kuma Al Istiqama suka shirya.

Sultan Abubakar, ya ce an buga littattafan a cikin harsunan Ingilishi da Larabci da Hausa.

Ya bayyana cewa, baje kolin kayayyakin tarihi na Afirka zai taimaka wajen dawo da martabar ‘yan Afirka da kimarsu a nan gaba.

Labarai Masu Nasaba

Gwamna Yusuf Ya Nuna Jin Daɗinsa Kan Yadda Kano Ta Zarce Legas, Oyo A Sakamakon NECO Na 2025

Sojoji Sun Tarwatsa Wata Haramtacciyar Masana’antar Ƙera Makamai A Filato

“Shugabannin Halifanci kadai sun yi rubuce-rubuce sama da 300 kan ayyukan diyar Shehu Usman Danfodio, Nana Asma’u da wasu dalibansa irin su AbdulKadir zul Mustapha. Wadannan ayyuka sun shafi batutuwa da dama daga sanannun masana kimiyyar Musulunci na tafsirin Alkur’ani, ilimin zamantakewa, tattalin arziki, kimiyyar siyasa da likitanci.

“Ya zuwa yanzu mun gyara tare da buga littattafai sama da miliyan 3.2 na ayyuka 200 na wadannan manyan shugabanni kuma sun zagaya kasa da dakunan karatu na daidaikun mutane da makarantu a fadin duniya.

“Wadannan littafai an buga su cikin harshen Turanci da Larabci da Hausa ne kuma insha Allahu a karshen wannan taro zan kawo wasu daga cikin wadannan littattafai. Muna cikin zamanin da turawan mulkin mallaka suka boye wadannan ayyuka ta hanyar kin sanya su cikin tsarin karatun makarantun gwamnati don wasu manufofi nasu

“Amma mun kudiri aniyar fito da wadannan ayyuka na ilimi don sanya su cikin harsunan da za su ba da damar yin amfani da su. Ya kuma kamata taron ya taimaka wajen gano abubuwan da muka gada don ganin sun shiga duniya.”

Shugaban taron, Farfesan tarihi kuma tsohon mataimakin shugaban Jami’ar Jihar Adamawa, Farfesa Al Kasum Abba ya ce babu wani abu da ya wuce tallafin karatu domin babu wata kungiya da za a iya tafiyar da ita bisa jahilci.

“Abin farin ciki ne cewa wannan taro yana gudana ne kan ilimin Musulunci da karatu a Afirka. Mutane ba su gane cewa tun kafin Turanci ya zo akwai ilimi a Musulunci. Idan aka nutsa cikin tarihi, ilimin Musulunci a Afirka yana da matukar muhimmanci.

“Jihadin Sakkwato wani yunkuri ne na zamantakewa amma Turawan Ingila sun zo suka kira shi da jihadin Fulani saboda suna son kafa tasu daular. Ba ma yin karatu ba, amma muna tsara guraben karatu na Musulunci yadda ya kamata a tsara shi. Sarkin Musulmi da Shehun Borno ya kamata su taimaka wajen samar da kudade don nazarin jihadin karni na 19 domin ya dauki matakai daban-daban na jihadin Sakkwato da Borno. Haka kuma muna bukatar kudi don fassara duk rubuce-rubucen karni na 19 domin mu fahimci tarihin al’ummarmu.”

Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna, wanda shi ne babban mai masaukin baki, ya ce taron ya zoa kan gaba kuma ya dace wajen bayyana irin gudunmawar da al’ummar Musulmi ke bayarwa ga ilimin duniya.

Gwamnan ya yi nuni da cewa, Daular Sakkwato na kan gaba wajen bayar da gudunmawar ilimi a Afrika. Ya ce Sheikh Usman Bin Fodio da dan uwansa Sheikh Abdullahi Fodio sun bayar da gudunmawa a fannonin jagoranci na dabi’a, ilimi, noma da kasuwanci.

Sani ya bayyana fatan taron zai samar da wani tsari na sake farfado da ilimin Addinin Musulunci domin ya dace da yanayin duniya wajen bai wa matasa dabarun rayuwa, tare da jaddada cewa yana da kyau a samar wa matasa sana’o’in da za su ba su damar yin takara a duniya da kuma bayar da gudunmawa mai ma’ana ga al’umma.

Taron dai ya samu halartar malaman Addinin Musulunci da masu bincike da masana daga sassa daban-daban na Afirka da ma duniya baki daya.

Daga cikin manyan baki sun hada da Shehun Borno, Alhaji Umar Garbai el-Kanemi, mataimakin gwamnan Jihar Kano, Alhaji Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda ya wakilci gwamna Abba Kabir Yusuf.

Sauran sun hada da Dokta Usman Bugaje, babban daraktan IRCICA, Mahmud Erol Kilic, babban sakataren kungiyar OIC, Hissein Brahim Taha ya samu wakilcin daraktan kula da harkokin al’adu, mataimakin shugaban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ya samu wakilcin mataimakin shugaban hukumar, Farfesa Ibrahim Dogo.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: KadunaLittattafaiMasanaSakkwatoSarkin MusulmiTaron Koyon Addinin Musulunci
ShareTweetSendShare
Previous Post

An Daure Wata Mata Kan Yi Wa Yaro Dan Shekara 8 Fyade

Next Post

Masarautar Zazzau Ta Soke Hawan Dabar Babbar Sallah

Related

NNPP
Manyan Labarai

Gwamna Yusuf Ya Nuna Jin Daɗinsa Kan Yadda Kano Ta Zarce Legas, Oyo A Sakamakon NECO Na 2025

8 hours ago
An Damke Basarake Da Wasu Mutum 10 Bisa Zargin Hada Baki Da ‘Yan Bindiga A Kudancin Kaduna
Manyan Labarai

Sojoji Sun Tarwatsa Wata Haramtacciyar Masana’antar Ƙera Makamai A Filato

10 hours ago
Yadda Ribas Ta Yi Cikar Ƙwari Yayin Da Gwamna Fubara Ya Koma Ofis
Manyan Labarai

Yadda Ribas Ta Yi Cikar Ƙwari Yayin Da Gwamna Fubara Ya Koma Ofis

16 hours ago
Tinubu Ya Gaza Wajen Magance Matsalar Tsaro A Nijeriya — Atiku
Manyan Labarai

Tinubu Ya Gaza Wajen Magance Matsalar Tsaro A Nijeriya — Atiku

17 hours ago
Sojoji Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Kashe Shugaban IPOB
Manyan Labarai

Sojoji Sun Cafke Babban Kwamandan IPOB

20 hours ago
Gwamnatin Tarayya Ta Dawo Da Karatun Tarihi A Makarantu
Manyan Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Dawo Da Karatun Tarihi A Makarantu

1 day ago
Next Post
Masarautar Zazzau Ta Soke Hawan Dabar Babbar Sallah

Masarautar Zazzau Ta Soke Hawan Dabar Babbar Sallah

LABARAI MASU NASABA

An Yi Bikin Tunawa Da Ranar Kaddamar Da Yakin Kin Mamayar Dakarun Japan A Birnin Shenyang

An Yi Bikin Tunawa Da Ranar Kaddamar Da Yakin Kin Mamayar Dakarun Japan A Birnin Shenyang

September 18, 2025
Likitocin Sin Dake Aikin Agajin Kiwon Lafiya A Nijar Sun Gudanar Da Tiyatar ALT A Karon Farko A Yammacin Afirka

Likitocin Sin Dake Aikin Agajin Kiwon Lafiya A Nijar Sun Gudanar Da Tiyatar ALT A Karon Farko A Yammacin Afirka

September 18, 2025
Fim Mai Taken 731 Na Tunatar Da Jama’a Muhimmancin Kiyaye Zaman Lafiya

Fim Mai Taken 731 Na Tunatar Da Jama’a Muhimmancin Kiyaye Zaman Lafiya

September 18, 2025
Kotun Sojin Nijeriya Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Wani Soja Da Ya Kashe Ɗan Adaidaita

Kotun Sojin Nijeriya Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Wani Soja Da Ya Kashe Ɗan Adaidaita

September 18, 2025
Sashen Raya Kimiyya Da Fasaha Na Sin Ya Kai Babban Matsayi Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Karo Na 14

Sashen Raya Kimiyya Da Fasaha Na Sin Ya Kai Babban Matsayi Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Karo Na 14

September 18, 2025
Jose Mourinho Ya Zama Sabon Kocin Benfica

Jose Mourinho Ya Zama Sabon Kocin Benfica

September 18, 2025
An Bude Taron Dandalin Tattauna Batun Tsaro Na Xiangshan Karo Na 12 A Birnin Beijing

An Bude Taron Dandalin Tattauna Batun Tsaro Na Xiangshan Karo Na 12 A Birnin Beijing

September 18, 2025
NNPP

Gwamna Yusuf Ya Nuna Jin Daɗinsa Kan Yadda Kano Ta Zarce Legas, Oyo A Sakamakon NECO Na 2025

September 18, 2025
Shugaban Guinea-Bissau Ya Goyi Bayan Shawarar Tsarin Shugabancin Duniya Da Sin Ta Gabatar

Shugaban Guinea-Bissau Ya Goyi Bayan Shawarar Tsarin Shugabancin Duniya Da Sin Ta Gabatar

September 18, 2025
An Damke Basarake Da Wasu Mutum 10 Bisa Zargin Hada Baki Da ‘Yan Bindiga A Kudancin Kaduna

Sojoji Sun Tarwatsa Wata Haramtacciyar Masana’antar Ƙera Makamai A Filato

September 18, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.