Shahararren mai amfani da kafar sada zumunta ta Tik Tok, Al’ameen G Fresh, ko kuma ‘Kano State Material’ kamar yadda wasu suka sanshi, ya yi wani bayani a shafinsa na Tik Tok wanda yake da mabiya fiye da mutum dubu 650, inda yake bai wa duk wani wanda ya taba batawa rayuwa hakuri dalilin abubuwan da yake dorawa a shafin nasa.
“Ina matukar bai wa duk wani wanda na batawa rai a wannan kafar ta Tik Tok musamman musulman Duniya hakuri, na kuma yi alkawarin daina duk wasu abubuwan da zasu bata rayuwar masoyana na wannan kafa, hakazalika, bayan ganawa da manyan malaman addinin musulunci, na yanke shawarar komawa makarantar Islamiyya inda zan dinga zuwa sau uku a duk sati.” In ji G Fresh.
- Rikita-rikitar Sauka Da Komawar Sheikh Daurawa Shugabancin Hisbar Jihar Kano
- An Sulhunta Gwamnan Kano Da Sheikh Aminu Daurawa
Ya kara da cewa, “babban malamin addinin musulunci kuma shugaban hukumar Hizba ta Jihar Kano, Malam Aminu Ibrahim Daurawa ne ya dauki nauyin wannan karatu da zan fara, inda ya biya duk kudaden da ake bukata domin in fara zuwa makarantar ta Islamiyya.”
A kwanakin baya dai hukumar ta Hizba a karkashin jagorancin shugabanta, Malam Aminu Ibrahim Daurawa ta gayyace Al’ameen (G Fresh) zuwa babban ofishinta da ke birnin Kano, domin amsa wasu tambayoyi.