Jama’a sun fara bayyana shakku dangane da yadda a ‘yan kwanakin nan ake fuskantar barazanar dawowar hare-haren mayakan kungiyar Boko Haram a jihohin Borno da Yobe, a daidai lokacin da ake tsammanin an raka bako; ashe yana labe a bayan gari.
Hakan ya biyo bayan wasu munanan hare-haren da mayakan ke ci gaba da aiwatar wa a wasu sassan jihohin biyu, wadanda suka dade suna fada da rikicin wanda ya jawo asarar dimbin rayukan al’umma tare da barnata dukiya ta biliyoyin naira; baya ga raunata dubban jama’a.
- Zulum Ya Daukaka Darajar Kwalejin Larabci Zuwa Babbar Cibiyar Yaki Da Akidun Boko Haram
- ISWAP Ta Hallaka Kwamandan Boko Haram A Sambisa
Cikin kasa ga wata daya, mayakan sun aiwatar da munanan hare-haren da suka jawo salwantar rayuka sama da 50, wanda a makon da ya gabata, mayakan sun kashe kimanin mutum 40 a kauyen Nguro-kayya dake karamar hukumar Gaidam a jihar Yobe, baya ga halaka wani jami’in hukumar hana fasa kauri ta Nijeriya a garin na Gaidam.
Yayin da a cikin wannan makon, mayakan na Boko Haram sun halaka manoman shinkafa 13, a cikin wani sabon harin d suka kai a kauyukan Karkut da Koshebe dake cikin karamar hukumar Mafa a jihar Borno.
LEADERSHIP Hausa ta zanta da wani magidanci daga garin Gaidam (bai aminta a bayyana sunan sa ba) a jihar Yobe, ya ce: “Zancen a ce babu Boko Haram bai taso ba, saboda kusan kana fita daga garin Gaidam kadan; ta bangaren gabas da Arewaci, za ka ci karo da yan Boko Haram, wanda tun a wancan lokacin su suke karbar haraji a hannun mazauna kauyuka.”
“Gaskiyar magana ita ce, har yanzu akwai sauran rina a kaba, saboda har yanzu yaran nan (Boko Haram) suna nan a kauyuka, ba sa jin tsoro ko shakkar wani mutum. Suna nan a cikin tsaunuka da dazuka tare da wasu kauyuka.”
“Kuma abin da ya sa ba a jin diriyarsu a lokacin damina shi ne gittawar ruwan Kogin Kumadugu, amma da zaran ya yanke za kana ganin su. Musamman tun daga gabashin Gaidam har zuwa Tafkin Chadi, wanda ana iya cewa sun mayar da yankin tamkar daularsu. Babu abin da mutum zai yi har sai da izinin su tare da biyan haraji.” Ya bayyana.
Shi ma wani bawan Allah da wakilinmu ya tattauna da shi ta wayar tafi da gidanka (bai yarda na bayyana sunan shi ba, saboda yanayin tsaro) a Yadin-Buni dake jihar Yobe, ya bayyana cewa, “ba zan ce ba a gama da Boko Haram ba, to amma gaskiyar magana shi ne an kashe maciji ba a sare kansa ba. Saboda har yanzu akwai yankunan da ba ma shiga a nan.”
“Idan ba ka manta ba, a kwanan baya ma sun yi wa wasu matasanmu sama da 10 kwanton-bauna, inda suka halaka su har lahira. Sannan har yanzun nan da nake magana da kai, kowane lokaci a cikin fargaba al’ummar kauyukanmu suke; saboda kowane lokaci zaman dar-dar ake.” In ji shi.
Jama’a da dama a wadannan jihohin suna ci gaba da bayyana ra’ayoyi daban-daban dangane da sabbin hare-haren tare da bayyana cewa ya kamata gwamnati ta sake nazarin matakan da ta bi wajen karbar tuban wasu daga cikin mayakan Boko Haram da ta yi a baya, inda ra’ayoyin ke nuni da cewa sai da dan gari a kan ci gari.