Manchester City ta tsallake rijiya da baya a gidan Orient, bayan ta doke su da ci 2-1, hakan ya sa ta tsallaka zuwa zagaye na biyar na gasar cin kofin FA ranar Asabar. Kamar kullum, Kevin De Bruyne ne ya fitar da kitse daga wuta ana gab-da za a tashi daga wasan.
Mai tsaron ragar Manchester City, Stefan Ortega ne ya ci gida tun a minti na 16 da fara wasan, sabon dan wasan City Khusanov ne ya ci kwallonsa ta farko bayan dawowa daga hutun rabin lokaci kafin Kevin De Bruyne ya jefa ta biyu.
Mutanen Guardiola kuwa su na matsayi na hudu a gasar Firimiya, hakazalika za su hadu da zakarun Turai, Real Madrid a gasar zakarun Turai a ranar Talata.














