Mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Dabid De Gea, ya wakilci kungiyar a wasanni 400 a gasar firimiyar Ingila a ranar Lahadi a wasan Manchester United ta ci Leeds United 2-0 a wasan mako na 23 a gasar Premier League a filin wasa na Elland Road.
Manchester United ta fara cin kwallo ta hannun dan wasan ta Marcus Rashford, sannan matashin dan wasa Alejandro Garnacho ya kara kwallo ta biyu minti biyar tsakanin kwallon Rashford.
- Abin Da Ya Sa Manoma Suka Ki Sayar Wa Da ‘Yan Kasuwa Amfanin Gonakansu
- Kamfanin Tsabtace Abinci Na Amurka Ya Dauki Yara Sama Da 100 Aiki Masu HadariÂ
Mai tsaron raga Dabid de Gea ne ya tsare ragar United, kuma wasa na 400 da ya yi kenan a Premier League sannan ya zama dan wasa na farko da ba dan Birtaniya ba da ya yi wasa da yawa a babbar gasar ta Ingila a tarihi.
De Gea ya tsare raga sau 139 da kwallo bai shiga ragarsa ba, an kuma yi nasara 216 da shi a United da shan kashi a fafatawa 87 sannan cikin wasanni 400 da ya yi, kwallo 431 ce ta shiga ragarsa a Premier League da yin kuskuren da aka ci United karo 16, ya kuma ci gida sau daya.
Tsohon mai tsaron ragar na tawagar Sifaniya ya hana kwallo 119 ya shiga ragarsa wato Sabes da tare fenariri hudu kuma De Gea ya lashe Premier League a kakar wasa ta 2012 zuwa 2013 sannan ya karbi kyautar dan wasan da yafi taka rawar gani a watan Janairun shekarar 2022.
Sannan shi ne ya lashe kyautar safar hannu ta zinare a matakin ba kamarsa a yin bajinta a kakar wasa ta 2017 zuwa 2018, har ila yau, De Gea mai shekara 32 ya karbi katin gargadi sau shida a wasannin Premier League, wanda ba a taba yi wa jan kati ba a gasar.
Ya koma Manchester United a kan kudi fam miliyan 19 daga Atletico Madrid
a shekarar 2011, tun daga lokacin ya zama na daya a tsare ragar United
kawo yanzu duk da kalubalen da yake fuskanta.