Jami’ar Turai da ke Amurka (EAU) ta fitar da sanarwa kan takardar shaidar digirin girmamawa da aka bai wa fitaccen mawaki Dauda Rarara, inda ta ce, takardar bogi ce kawai, babu wanda aka ba izinin gabatar da irin wannan taron.
A wani biki da ya samu halartar manyan baki da suka hada da gwamnan jihar Katsina Dikko Radda a otel din ‘Nicon Luxury’ Abuja a ranar Asabar din da ta gabata, wasu mutane da suka bayyana kansu a matsayin wakilan jami’ar sun karrama Rarara da wasu da Digirin girmamawa.
- Djed Spence: Musulmin Da Ya Fara Bugawa Tawagar Ingila Wasan Ƙwallon Ƙafa A Tarihi
- Tinubu Bai Shirya Yin Gaskiya A Zaɓen 2027 —Buba Galadima
Amma a cikin wata sanarwa da aka buga a shafin intanet din jami’ar, cibiyar ta nesanta kanta da Rarara da jami’an da suka bayyana kansu a matsayin wakilan jami’ar.
“Sanarwar jan hankaki – Taron bogi ‘convocation’ a Nijeriya – Jami’ar ba ta ba Dauda Kahutu Rarara digirin girmamawa ba”.
A yau (Lahadi) ne aka sanar da Jami’ar EAU labarin wani biki da kafafen yada labarai na Nijeriya suka rahoto ƙaryar cewa, Jami’ar ta gudanar da wani taro a ranar Asabar a Hotel din ‘NICON Luxury’ Abuja, Nijeriya.
Jami’ar ba ta ba da izinin gudanar da wani taro a wannan wuri a ranar ba, kuma an shirya wannan taron ne ta hanyar damfara ba tare da sanin ko izinin Jami’ar ba. Waɗanda suka shirya wannan taron sun yaudari wasu da yardar cewa suna wakiltar Jami’ar EAU, amma wannan gaba ɗaya ƙarya ce kuma ba su da ikon yin hakan, ko kuma karɓar kuɗi a madadin Jami’ar.
Jami’ar EAU ba ta ba Dauda Kahutu Rarara, Alhaji Ahmed Saleh jnr, Mustapha Abdullahi Bujawa da Tarela Boroh digirin girmamawa ba. Duk masu riƙe da digiri daga Jami’ar, za a iya samun sunansu kamar yadda aka jera a cikin Rajista na Digiri a https://europeanamerican.university/about/register-of-graduates
An ambaci sunan Musari Audu Isyaku a matsayin “Wakilin Arewacin Nijeriya na jami’ar”. Wannan mutumin ba shi da ikon wakiltar Jami’ar EAU kuma wannan taron da ya shirya, da bayar da digirin girmamawar duka ƙarya ce.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp