Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda, ya bayar da kyautar Naira miliyan 278 ga Alhazan jihar a kasar Saudiyya.
Hakan ya fito cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai ranar Litinin a Katsina, ta hannun babban sakataren yada labaran gwamnan, Malam Ibrahim Kaula.
- Cikin Alhazan Nijeriya An Samu Masu Larurar Kwakwalwa Da Masu Juna Biyu
- Hajji 2023: Tinubu Ya Bukaci Alhazai Da Su Kara Hakuri Da Halin Matsi Da Takura Da Suke Ciki
A cewarsa, Amirul Hajj na jihar kuma tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Katsina, Alhaji Tasiu Musa-Maigari, ya bayyana hakan a Makkah a ranar Lahadin da ta gabata lokacin da ya ziyarci maniyyatan.
Musa-Maigari ya ci gaba da cewa, Radda ya kuma bukaci alhazai da su yi addu’ar Allah ya kawo karshen rashin tsaro a jihar.
Ya kara da cewa gwamnan ya umarce shi da ya mika gaisuwar Sallah da taya alhazai murnar kammala aikin Hajjin da suka yi.
Daga baya tsohon shugaban majalisar ya sanar da bayar da gudummawar Riyal 300 (daidai da N6O,000) da gwamnan ya baiwa kowane mahajjaci a matsayin alawus na ciyarwa.
Tun da farko, Sakataren zartarwa na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Katsina, Alhaji Suleiman Kuki, ya bayyana jin dadinsa da yadda alhazan jihar ke gudanar da dabi’u nagari a yayin gudanar da aikin hajjin na wannan shekara.
A cikin tawagar Amirul Hajjin akwai tsoffin mataimakan gwamnonin jihar, Alhaji Abdullahi Garba-Faskari, Alhaji Abdullahi Garba Aminci, da shugaban hukumar, Magajin Garin Katsina.