Hukumar lura hanya da rage cunkoson ababen hawa ta jihar Kano (KAROTA) ta kama wani direba (ba a bayyana sunansa ba) bisa zargin karya dokokin ababen hawa da murƙushe furannin da gwamnatin jihar ta dasa a babban titin birnin Kano.
Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis a titin Murtala Muhammad dake cikin birnin Kano, inda aka ruwaito direban ya ketare daga inda bai dace ba zuwa titin kuma ya murƙushe sabbin furannin da aka dasa.
- KAROTA Ta Kama Matasa 5 Kan Ɗaukar Bidiyo A Kan Hanya A Kano
- Tuƙin Ganganci: Direba Ya Kashe Jami’in KAROTA
Mai magana da yawun KAROTA, Abubakar Ibrahim Sharada, ya tabbatar da kama direban, inda ya ce za a gurfanar da shi domin zama izina ga sauran direbobi.
Sharada ya kuma gargaɗi direbobi da su kiyaye dokokin hanya, yana mai cewa hukumar ba za ta lamunci lalata dukiyar gwamnati ba.














