Shugaban bankin shigo da kayayyaki da fatirwa na Afrika (African Export and Import Bank), kuma shugaban rukunin daraktocin bankin Farfesa Benedict Oramah, yace Nijeriya ta fada matsalar tattalin arziki ne sakamakon dogaro da man fetur wajan samun kudaden shiga.
Ferfesan ya bayyana haka lokacin da yake jawabi a Yola, lokacin bukin yaye dalibai karo na 14 da jami’ar Amurka a Nijeriya (AUN), ta gudanar.
- Fintiri Ya Rantsar Da Mace Ta Farko Babbar Mai Shari’a A Adamawa
- ‘Yansanda Sun Damke Wani Mutum Da Ya Kashe Matarsa A Adamawa
Benedict ya ce, yawan jama’ar kasar sunfi karfin dogaro kan abu guda daya su rayu. Ya bukaci dalibai da suka kammala karatun da su yi amfani da kwarewar da suka koya lokacin karatunsu su gina kasar, ta zama kasa ce mai sarrafawa da fitar da kayayyaki.
Ya ci gaba da cewa “juyin juya hali gagarumin zango ne, ‘yancin wannan kuma ana koyar da shi ne, wannan aikin fasaha da ra’ayoyi ne da aiki tukuru da zuba jari.
“Hazikanci ya na kai mutum ga muhimmin abu na asali da canja yanayin duniyarmu, daga tsohon zato da sake inganta rayuwarmu.
“Kuma cikin aminci da masana’antu da koyarwa da raya cibiyoyin kasuwanci, mai makon daukar makamai, yaki za a koyar amma ba yakin soja ba, dabaru ba albarushi ba, karfafawa ake bukata domin habaka tattalin arzikinmu” inji Farfesa Oramah.
A nasa jawabin, mukaddashin jami’ar Dakta Attahiru Yusuf, ya yabawa wanda ya kafa makarantar, tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, ya ce jami’ar ta samar muhimman mutane da kayayyakin aiki ga kasashen Afrika da duniya baki daya.
Ya ce dalibai 234, jami’ar ta yaye a bikin na bana (2023). Wasu daga cikin manya baki mahalarta taron sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abunakar da gwamana Ahmadi Umaru Fintiri, Dakta Usman Bugaji da dai sauransu.