Babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Lateef Fagbemi, ya ce gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kafa dokar masu fallasa barayin gwamnati, saboda ana shirin dawo da kudirin dokar a zauren majalisa ta 10.
Ya bayyana haka ne a wani taro da kungiyar ci gaban al’umma (PRIMORG) tare da hadin gwiwar cibiyar yada labarai da wayar da kan jama’a ta Afrika (AFRICMIL) suka shirya a Abuja.
- Gwamna Radda Ya Yi Allah Wadai Da Hare-haren ‘Yan Fashin Daji A Jihar Katsina
- NLC Da TUC Sun Rufe Titin Zuwa Filin Jirgin Saman Abuja, Sun Bukaci A Hana Zuwa Imo
Wannan na zuwa ne gabanin wani taron sake fasalin tsarin dokar kariya ga masu fallasa barayin gwamnati da zai gudana a Abuja.
Ministan shari’ar wanda ya samu wakilcin babban jami’in ma’aikatar shari’a, Adesoji Afolabi, ya jaddada cewa za a dawo da kudirin dokar fallasa barayin gwamnati da bai samu karbuwa ba a zauren majalisa ta tara, sannan a mika shi ga majalisar zartarwa ta tarayya kafin zuwa majalisar kasa.
Afolabi ya ce majalisar da ta shude ba ta iya zartar da kudurin dokar fallasa barayin gwamnati ba saboda karancin lokaci, amma ya a wannan karon yana da kwarin gwiwa cewa doka za ta fara aiki gadan-gadan.
Ministan ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya da su mara wa kokarin gwamnati baya na yaki da cin hanci da rashawa tare da jinjina wa kungiyoyin AFRICMIL, PRIMORG da sauran kungiyoyin fararen huda da suka ba da nasu gudummuwa ga dokar.
Ko’odineta na AFRACMIL, Dakta Chido Onumah ya bayyana cewa dokar fallasa barayin gwamnati za ta yi matukar tsaftace gwamnatin Shugaba Bola Tinubu idan ta samu nasara.
Ya kara da cewa ’yan Nijeriya masu son fallasa ayyukan cin hanci da rashawa za su samu kariya ta musamman a karkashin wannan doka.