Biyo bayan dokar da Hukumar tabbatar da ingancin makarantu ta jihar Kaduna (KSSƘAA), ta sanyawa makarantu masu zaman kansu dangane da matsalar yawaitar ƙara ku ɗaɗan makaranta ba bisa ƙa’ida ba da kuma ƙara litattafan ɗalibai da dai sauransu Manufar dokar ita ce, inganta ingancin koyarwa da kuma kare haƙƙin ɗalibai da iyayensu.
A kwanan baya ne hukumar tabbatar da ingancin makarantu ta jihar Kaduna (KSSƘAA), ta gargaɗi masu makarantu masu zaman kansu kan ƙara kuɗin makaranta ba tare da samun amincewar gwamnatin jihar a hukumance ba.
A wata takarda mai kwanan ranar 7 ga Satumba, 2023, wacce Mercy Bainta Kude, Daraktar Sashen Makarantu masu zaman kansu ta sanya wa hannu a madadin Darakta-Janar, Hukumar ta jaddada Tewa “babu wani ko wata mai makaranta da zai ko za ta ƙara kuɗin makaranta ko inganta makarantar ba tare da amincewar KSSƘAA ba. Ƙarin kuɗin makarantu a irin Wannan zagon karatun wato zagon na karatu yana ciwa iyaye tuwo a ƙwarya musamman ganin lokacine da ake biyan kuɗin makarantar ɗalibai da sayan littafan karatu lamarin da sanya wasu makarantu yin amfani da wata dama wajen ƙara kuɗin makaranta ba bisa ƙa’idaba.
- Dawowa Hutu Ya Tayar Da Hankalin Iyaye Saboda Ƙarin Kuɗin Makaranta
- Gwamnatin Bauchi Ta Cire Shugaban Makaranta Kan Satar Kayan Gwamnati
Hakazalika , masana harkar ilimi Sunce matakin kafa dokoki masu tsauri kan makarantun masu zaman kansu yana fuskantar barazana da ƙalubale iri-iri, musamman tun bayan sanarwar kwanan baya na hana ƙara kuɗin makaranta ba tare da amincewa daga gwamnati ba.
Duk da cewa akwai wasu ƙalubale, da dama daga cikin jama’a na goyon bayan wannan doka.
Muhawara game da sanya doka a kan makarantu masu zaman kansu yana ta ci gaba a ciki da wajen jihar Kaduna saboda ƙaruwar makarantun masu zaman kansu a cikin ƴ an shekarun nan musamman a cikin sabbin unguwanni da ke cikin ƙwaryar Kaduna.
Abubuwan da jama’a ke magana a kai sun haɗa da tabbatar da inganci, kare haƙƙoƙin ɗalibai, da daidaita kuɗaɗe.
Masu mallakar makarantun masu zaman kansu sun koka da yawan haraji da tsadar aiki, wanda ya sa su yi tsayin daka wajen ƙara kuɗin makaranta.
Sanya doka mai tsauri na iya ƙara musu nauyi kuma ya tilasta wasu rufe makarantunsu.
Sai dai masana harkar ilimi Sun bayyana cewa daidaitawa da haɓaka inganci: dokar za ta sa makarantu masu zaman kansu su bi ƙa’idojin koyarwa na jihar Kaduna, wanda hakan zai inganta ingancin ilimi ga kowa.
Hakazalika, dokar za ta taimaka wajen kare iyalai daga biyan kuɗi mai tsoka da kuma tabbatar da cewa suna samun ilimi mai inganci a farashi mai sauƙi Hasalima, da yawa daga cikin wadannan makarantun wato makarantu masu zaman kansu suna da ƙarancin inganci saboda suna ɗaukar ma’aikatan da ba su da cikakkiyar horo saboda rashin son biyan su albashi mai tsoka.
Wannan matsala na tattare da ingancin ilimi ga zalibai. Da dama daga cikin makarantun masu zaman kansu ba su da kayan aiki da ya kamata, kamar ɗakunan karatu da ɗakunan gwaje-gwaje. Wasu daga cikinsu suna amfani da gine-gine masu haɗari da ba a duba ingancinsu ba, wanda hakan yana haifar da haɗari ga ɗalibai.
Hakan ya sanya da dama daga cikin jama’a na goyon bayan dokar da gwamnatin jihar Kaduna ta sanya; suna ganin cewa hakan zai daidaita ingancin koyarwa da kuma sa makarantu su riƙa bin ƙa’idoji.
Binciken leadership Hausa ya gani cewa wasu masu makarantun masu zaman kansu sun nuna damuwa game da dokar, suna jin cewa hakan zai ƙara musu nauyi da kuma rage musu damar samun riba.
Ɗaya daga cikin manyan ƙalubale shi ne rashin iya sa ido kan makarantun masu zaman kansu. Akwai haɗarin cin hanci da rashawa, wanda zai iya sa a yi watsi da ƙa’idoji.
Wasu na cewa dokar ba za ta iya magance matsalar ingancin koyarwa ba, matuƙar gwamnati ba ta inganta makarantun ta na gwamnati ba.
A zantawar da Wakilinmu da wasu iyaye Sun bayyana hamsuwarsu dangane da Wannan dokar inda suka sanya dokar tazo a daidai lokacin da ake buƙata.
Hakazalika, Sunce muddin gwamnatin jihar Kaduna Tana son ɗorewar dokar sai ta Samar da Jami’ai waɗanda zasu rinƙa biybiyar makarantun domin tabbatar da dokar Tana aiki yadda ya kamata.
Wasu makarantun da wakilinmu ya Kai ziyara a ƙananan hukumomin Kaduna ta Arewa da ta Kudu da kuma ƙaramar hukumar Igabi wacce tafi kowacce ƙaramar hukuma yawan makarantu masu zaman kansu Sun bayyana cewa idan wannan dokar ta ɗore kuma basu samu Tallafin gwamnatin ba babu shakka akwai yiwuwar durƙushewar makarantu da yawan gaske duba da ganin cewa kuɗaɗan da ɗalibai suke biya dana sayar da littafai sune suke riƙe makarantun suna masu cewa rashin samun hakan zai haifar musu da ƙalubale mai tarin yawa.
Wani mamallakin wata makaranta a garin Hayin Rigasa da Unguwar Kawo sun tabbatarwa da wakilinmu cewa a haƙiƙanin gaskiya basa goyon bayan Wannan dokar muddin ba za’a basu damar ƙara ɗudin makaranta inda suka ce ƙarin kuɗin man fetur shi kaɗai ya cancanci wasu makarantun su ƙara kuɗinsu domin suma malaman da suke koyarwa Sun samu ƙarin kuɗin abun hawa Wanda dole a ƙara musu albashi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp