• English
  • Business News
Friday, September 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dokar Haraji Ta Gwamnatin Tinubu Za Ta Illata Arewa

by Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
10 months ago
in Manyan Labarai
0
Dokar Haraji Ta Gwamnatin Tinubu Za Ta Illata Arewa
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Sabuwar dokar sake fasalin haraji da Shugaba Bola Tinubu ya aikawa majalisar kasa domin amincewa a matsayin doka ta tayar da kura tare da tayar da jijiyar wuya musamman kan illar da za ta yi wa muradun Arewa da al’ummar ta hanyar fifita jihar Lagas sama da daukacin jihohi.

Kungiyar gwamnonin Nijeriya, kungiyar gwamnonin Arewa da jigogin siyasar Arewa da kungiyoyi masu zaman kan su tuni sun yi Allah – wadai da dokar tare da kira ga majalisar kasa da ta yi watsi da dokar.

  • Ko Shakka Babu Tinubu Ne Zai Lashe Zaben Shugaban Kasa A 2027 – APC
  • Dambarwar Shirin Tinubu Na Yi Wa Dokar Haraji Kwaskwarima…

Kungiyar gwamnonin Arewa ta ce daya daga cikin kudurorin dokar bai yi daidai da muradun al’ummar Arewa da wasu bangarori na kasa ba, don haka ta tsaya kan rashin amincewa da dokar.

Wadanda ke sahun gaba wajen cece- kuce kan dokar da nuna rashin dacewarta a wannan lokacin, sun bayyana cewar a wannan tsari da ake a kai na mulkin dimokradiyya ya kamata a jingine maganar dokar har sai zuwa gaba a lokaci mafi dacewa da aiwatar da ita.

Kudurin dokar wadda Shugaba Tinubu ya aikawa majalisa a wata ta kunshi bangarori guda hudu da suka tayar da hazo wadanda suka hada da dokar harajn Nijeriya, dokar kafa hukumar kudaden shiga, daftarin kula da haraji da dokar da za ta bayar da damar kafa hukumar tattara kudaden haraji ta hadin guiwa.

Labarai Masu Nasaba

Nan Ba Da Jimawa Ba Hauhawar Farashin Kayayyaki Za Ta Zama Tarihi —Fadar Shugaban

Ce-ce-kuce Kan Shirin Ƙara Wa Ƴan Siyasa Masu Riƙe Da Madafun Iko Albashi

Sai dai duk da adawar da gwamnoni suka nuna ga dokar tare da kira ga majalisa da ta yi watsi da ita, fadar shugaban kasa ta bayyana cewar sam ba za ta jaye kudurin dokar ba sai dai ta yi mata gyare- gyare.

Gwamnonin jihohi 36 ne suka bukaci a jaye kudurin dokar, a cewarsu akwai bukatar kara tuntuba da jin ra’ayoyin al’umma kan dacewa ko rashin dacrwar dokar.

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ne ya bayyana matsayar gwamnonin Nijeriya a taron majalisar bunkasa tattalin arzikin kasa wanda mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya jagoranta a makon jiya.

Sai dai fadar shugaban kasa ta yi fatali da shawarar gwamnonin, ta jadadda cewar za a iya yin gyara a wasu sassan dokar a yayin da aka gabatar da dokar domin muhawara a majalisa wakilai da ta dattawa.

A bangaren ta, majalisar wakilai ta ce har yanzu ba ta cimma matsaya kan dokar da bangaren zartaswar gwamnati suka aika mata ba. Majalisar ta ce za ta bi diddigin dokar tare da cewar abubuwan da suka tayar da hazo a dokar suna nuna muhimmancin da suke da shi kuma cece- kucen da ake yi abu ne mai kyau a mulkin dimokuradiyya.

Shugaban majalisar, Tajuddeen Abbas wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin a wajen taron tattaunawa kan dokar a majalisa ya bayyana cewar za su tabbatar abubuwan da dokar ta kunsa sun yi daidai da muradun mazabun su da al’ummar kasa bakidaya wanda ya shafi gyare- gyare a inda ya kamata.

Majalisar ta ce dokar na da manufar hada kan kudaden harajin da kasa ke samu, karfafa daidaito da samar da ingantaccen yanayin zuba jari da kirkirar sababbin abubuwa. Ta ce wajibi ne a aiwatar da gaskiya da adalci a sha’anin haraji.

Gwamnatin tarayya dai ta hannun ofishin shugaban kwamitin sabuwar dokar harajn, Taiwo Oyedele ta bayyana cewar dalilin canza fasalin yadda ake karbar harajin shine domin a kawo karshen kalubale masu yawa irin harajin birane daban daban, rage nauyin harajin daga kan daidaikun wuraren kasuwanci da taimakawa kasuwanci da habaka tattalin arziki. Ya ce ko kadan babu wani abin fargaba, domin babu wani yanki da zai cutu a dalilin dokar.

A bisa ga cece- kucen da ake yi a majalisa kan dokar, mataimakin shugaban kwamitin yada labarai na majalisar wakilai, Philip Agbese ya bayyana cewar manbobin majalisar za su marawa kudurin dokar haraji ta Tinubu baya ta hanyar kin amincewa da bukatar gwamnoni ta watsi da dokar.

Agbese a zantawarsa da manema labarai ya bayyana cewar ‘yan majalisar na ganin kudurin dokar na da manufar bunkasa tattalin arziki don haka sun shirya aminta da duka bangarori hudu na kudurin.

Ya ce a kan dokar a yanzu haka gwamnoni na yi masu barazanar hana masu tsayawa takara a zaben 2027 idan har ba su jaye goyon bayansu ga dokar ba kuma a cewarsa muddin dokar na da manufar bunkasa tattalin arziki to ba za su jaye goyon bayan su ba.

A nasa bangaren shugaban kungiyar ‘yan majalisar yankin Arewa, Honarabul Alhassan Ado Doguwa ya bayyana cewar masu shata dokokin za su yi la’akari da muradun kasa wajen tabbatar da sabuwar dokar.

Ya bayyana cewar ba za su yi gaggawar aminta da dokar ba, ya ce za su tabbatar da gaskiya da adalci ga dokar da al’ummar Nijeriya ta hanyar nazarin dokar a tsanake kafin amincewa domin lamari ne da ya shafi rarraba haraji.

Haka ma jagoran jam’iyyar NNPP, kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Sanata Rabi’u Kwankwaso ya bayyana cewar jihar Lagas ce ake son fifitawa tare da durkusar da yankin Arewa.

Tsohon gwamnan Kano, ya zargi cewar a na kokarin durkusar da harkokin kasuwanci a Arewa tare da bunkasa tattalin arzikin Lagas ta hanyar mallake Arewacin Nijeriya. Ya ce akwai yunkuri mai karfi daga yankin Lagas na mallake bangaren Arewa.

Bangarorin da Arewa za su cutu a dokar sun hada da cire adadin mutane masu yawa da aka yi daga tsarin haraji domin dokar ta bayyana cewar “duk mutumin da ba ya karbar naira miliyan 2, 200 a matsayin albashi a shekara ba zai biya haraji ba, wanda hakan babban kalubale ne ga jihohi wadanda naira dubu 70 ne mafi karancin albashi wadanda a shekara 840, 000 ne.”

Hakan ya nuna cewar za a samu koma baya sosai ga kudaden da jihohi ke samu daga ma’aikatansu domin kudaden da za a samu a karshen shekara kalilan ne idan aka hada albashin su wanda hakan ne dalilin da yasa gwamnoni suka ki aminta da kudurin dokar.

Bugu da kari abubuwan da yankuna ke samarwa wadanda ake cire haraji a ciki na daga cikin abubuwan da suka tayar da kura a sabon fasalin dokar domin kuwa a bisa ga tsarin yankin Arewa na fama da matsalar karancin masana’antun da suka tsayu da kafafun su wadanda ke samar da haraji mai tsoka, babban abin da Arewa ke samarwa kasa bakidaya shine abinci kuma babu haraji a cikinsa.

LEADERSHIP Hausa ta labarto cewar a na raba kudaden kason tarayya da ake samu daga jihohi inda tarayya ke samun kashi 52 yayin da ake rabawa jihohi kashi 26, sai kananan hukumomin da ake rabawa kashi 20 a bisa la’akari da yawan al’ummar ko wace jiha.

Sabon kudurin dokar ya nuna a yanzu a na son a mayar da tsarin zuwa iya yawan abin da jiha ke samarwa a wata iya adadin abin da kowace jiha za ta samu daga gwamnatin tarayya a kowane wata.

Masana sun bayyana cewar a wani rabo da aka yi a watan Satumba, jihar Lagas ta samu naira biliyan 45 yayin da jihohin Kano da Kaduna suka samu naira biliyan 10 wanda a cewarsa hakan ba daidai ba ne.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Haraji
ShareTweetSendShare
Previous Post

Dambarwar Shirin Tinubu Na Yi Wa Dokar Haraji Kwaskwarima…

Next Post

Kujerar Ɗindindin A Majalisar Dinkin Duniya: Tinubu Na Kamun Ƙafa Wurin Shugabannin G20

Related

Nan Ba Da Jimawa Ba Hauhawar Farashin Kayayyaki Za Ta Zama Tarihi —Fadar Shugaban
Manyan Labarai

Nan Ba Da Jimawa Ba Hauhawar Farashin Kayayyaki Za Ta Zama Tarihi —Fadar Shugaban

2 hours ago
Ce-ce-kuce Kan Shirin Ƙara Wa Ƴan Siyasa Masu Riƙe Da Madafun Iko Albashi
Manyan Labarai

Ce-ce-kuce Kan Shirin Ƙara Wa Ƴan Siyasa Masu Riƙe Da Madafun Iko Albashi

3 hours ago
NNPP
Manyan Labarai

Gwamna Yusuf Ya Nuna Jin DaÉ—insa Kan Yadda Kano Ta Zarce Legas, Oyo A Sakamakon NECO Na 2025

15 hours ago
An Damke Basarake Da Wasu Mutum 10 Bisa Zargin Hada Baki Da ‘Yan Bindiga A Kudancin Kaduna
Manyan Labarai

Sojoji Sun Tarwatsa Wata Haramtacciyar Masana’antar Ƙera Makamai A Filato

17 hours ago
Yadda Ribas Ta Yi Cikar Ƙwari Yayin Da Gwamna Fubara Ya Koma Ofis
Manyan Labarai

Yadda Ribas Ta Yi Cikar Ƙwari Yayin Da Gwamna Fubara Ya Koma Ofis

23 hours ago
Tinubu Ya Gaza Wajen Magance Matsalar Tsaro A Nijeriya — Atiku
Manyan Labarai

Tinubu Ya Gaza Wajen Magance Matsalar Tsaro A Nijeriya — Atiku

24 hours ago
Next Post
Kujerar Ɗindindin A Majalisar Dinkin Duniya: Tinubu Na Kamun Ƙafa Wurin Shugabannin G20

Kujerar Ɗindindin A Majalisar Dinkin Duniya: Tinubu Na Kamun Ƙafa Wurin Shugabannin G20

LABARAI MASU NASABA

Haraji

2027: Su Wane Ne Ke Tsoron Guguwar Makinde A Jam’iyyar  PDP

September 19, 2025
Nan Ba Da Jimawa Ba Hauhawar Farashin Kayayyaki Za Ta Zama Tarihi —Fadar Shugaban

Nan Ba Da Jimawa Ba Hauhawar Farashin Kayayyaki Za Ta Zama Tarihi —Fadar Shugaban

September 19, 2025
Ce-ce-kuce Kan Shirin Ƙara Wa Ƴan Siyasa Masu Riƙe Da Madafun Iko Albashi

Ce-ce-kuce Kan Shirin Ƙara Wa Ƴan Siyasa Masu Riƙe Da Madafun Iko Albashi

September 19, 2025
An Yi Bikin Tunawa Da Ranar Kaddamar Da Yakin Kin Mamayar Dakarun Japan A Birnin Shenyang

An Yi Bikin Tunawa Da Ranar Kaddamar Da Yakin Kin Mamayar Dakarun Japan A Birnin Shenyang

September 18, 2025
Likitocin Sin Dake Aikin Agajin Kiwon Lafiya A Nijar Sun Gudanar Da Tiyatar ALT A Karon Farko A Yammacin Afirka

Likitocin Sin Dake Aikin Agajin Kiwon Lafiya A Nijar Sun Gudanar Da Tiyatar ALT A Karon Farko A Yammacin Afirka

September 18, 2025
Fim Mai Taken 731 Na Tunatar Da Jama’a Muhimmancin Kiyaye Zaman Lafiya

Fim Mai Taken 731 Na Tunatar Da Jama’a Muhimmancin Kiyaye Zaman Lafiya

September 18, 2025
Kotun Sojin Nijeriya Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Wani Soja Da Ya Kashe ÆŠan Adaidaita

Kotun Sojin Nijeriya Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Wani Soja Da Ya Kashe ÆŠan Adaidaita

September 18, 2025
Sashen Raya Kimiyya Da Fasaha Na Sin Ya Kai Babban Matsayi Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Karo Na 14

Sashen Raya Kimiyya Da Fasaha Na Sin Ya Kai Babban Matsayi Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Karo Na 14

September 18, 2025
Jose Mourinho Ya Zama Sabon Kocin Benfica

Jose Mourinho Ya Zama Sabon Kocin Benfica

September 18, 2025
An Bude Taron Dandalin Tattauna Batun Tsaro Na Xiangshan Karo Na 12 A Birnin Beijing

An Bude Taron Dandalin Tattauna Batun Tsaro Na Xiangshan Karo Na 12 A Birnin Beijing

September 18, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.