Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana adawarta da ƙudirin dokar haraji da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya aike wa majalisar dokokin Nijeriya.
Ta bayyana cewa dokar za ta ƙara jefa al’umma cikin wahala da talauci.
- Gwamnatin Kano Ta Yi Fatali Da Kudirin Sake Fasalin Dokar Haraji
- Dr. Maryam Yola Ta Zama Farfesa Mace Ta Farko Kan Magungunan Gargajiya Da Al’adun Hausa
Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda mataimakinsa Aminu Abdussalam Gwarzo, ya wakilta, ya bayyana haka ne a yayin bikin murnar shiga sabuwar shekarar 2025 da aka gudanar a Filin Mahaha da ke birnin Kano.
Sanarwar da mai magana da yawun mataimakin gwamnan, Ibrahim Garba, ya fitar ta bayyana cewa, “Wannan ƙudirin haraji ba zai taimaka wajen farfaɗo da tattalin arziƙinmu ba.
“Maimakon haka, zai ƙara tsananta wahalar da talakawanmu ke fuskanta. Gwamnatin Kano tana ƙin amincewa da wannan ƙudiri.”
Hakazalika, gwamnan ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta duba wannan ƙudiri da kyau, tare da sanya walwalar al’umma a gaba kafin yanke hukunci.
Ya ce akwai buƙatar kawo hanyoyin da za su rage matsin tattalin arziƙi maimakon ƙarin haraji da zai shafi mafi yawan talakawa.
Wannan martani na gwamnatin Kano ya zo ne a dai-dai lokacin da gwamnatin Bauchi ta yi irin wannan suka.
Gwamnan Bauchi, Bala Muhammad, ya bayyana cewa dokar harajin ba ta dace da halin da ake ciki ba kuma tana iya haddasa ƙarin matsin hankali tattalin arziƙi.
Wannan yana nuni da yadda lamarin ke ƙara haifar da cece-kuce tsakanin jihohi da gwamnatin tarayya.