ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, December 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dole A Hukunta Wadanda Suka Kai Harin Bom A Kaduna -Majalisar Dattawa

by Sulaiman
2 years ago
majalisar kasa

Majalisar Dattawan Nijeriya ta lashi takobin gudanar da bincike kan harin kuskuren da rundunar sojin kasar ta kai, da ya janyo mutuwar mutane da dama a Jihar Kaduna.

Kawo yanzu dai mutane da dama ne suka rasa rayukansu ba, yayin da kuma wasu ke kwance a gadon asibiti ana kula da lafiyarsu.

  • Yawan Yaran Da Ke Fama Da Cututtuka Masu Alaka Da Sassan Jiki Masu Taimakawa Numfashi Ya Ragu A Kasar Sin
  • Tinubu Zai Sake Fuskantar Wata Shari’ar A Kotun Koli Kan Zaben 2023

Sanata Lawal Adamu Usman, (Mr La), shi ne dan majalisar dattawan Nijeriya mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, inda aka kai harin, ya shaida wa BBC cewa al’amari ne da ba za su bari ya wuce ba:

ADVERTISEMENT

“Wannan abu ne da ba za mu bari ya wuce ba, za mu sa a bincika a gano dalilin da ya sa ake samun irin wannan iftila’i. Mutane na yin ibadarsu a zo a jefa mu su bam, sai mun binciko abin da ya faru kuma a dauki mataki akan wadanda suka kai harin” in ji shi.

Gomman mutane ake fargabar sun rasa rayukansu bayan harin bam da jirgin saman yakin ya kai wa gungun masu Mauludi bisa kuskure a kauyen Tudun Biri da ke Karamar Hukumar Igabi .

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Sai dai duk da cewa yanki ne da ke fama tashin hankali sakamakon hare-haren ‘yan bindiga amma majalisar dattawan Nijeriya ta danganta al’amarin kan gazawar sojojin kasar wajen tattara bayanan sirri kamar yadda sanata Lawal Adamu Usman ya ce:

“Akwai gazawa wajen tattara bayanan sirri saboda ba bu yadda za a yi ka saki harsashi idan baka tabbatar da wurin da za ka kai harin ba ballantana bam.

Bam babban abu ne kafin a sake shi dole sai an tabbatar da cewa masu garkuwa da mutane ne a wurin. Kuma idan har akwai sakaci to za mu tabbatar cewa an kama mutanen kuma za’a hukuntansu “, in ji shi.

Tun farko Gwmnatin Jihar Kaduna ta kafa kwamitin bincike da aka dorawa alhakin gano abin da ya faru.

Ita ma majalisar dattawan kasar ta ce za ta kafa kwamitin binciken akan alamarin tare da kai dauki ga mutanen da alamarin ya rutsa da su.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja
Manyan Labarai

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta
Manyan Labarai

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka
Ra'ayi Riga

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Next Post
Adadin Hatsin Da Aka Girbe A Sin A Bana Ya Kai Matsayin Koli

Adadin Hatsin Da Aka Girbe A Sin A Bana Ya Kai Matsayin Koli

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.