ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, October 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dole Afirka Ta Samar Da Hanyoyin Magance Matsalolinta

by Rabi'u Ali Indabawa
4 weeks ago
Afirka

Daga dogaro da kai zuwa hadin gwiwa, daga amfani da abin da aka samar zuwa samarwa da kanmu, sannan daga daidaita kanmu da abin da ake da shi zuwa mallakar abubuwan da muka samar. Afirka ba ta rasa dabaru, hazaka, kirkire-kirkire ko damar magance matsalolinta da kanta ba. Abin da galibi muka rasa shi ne yarda da jajircewa wajen samar da hanyoyin magance matsaloli wadanda aka tsara su yadda ya kamata bisa la’akari da halin da muke ciki, tare da ba su goyon bayan da suke bukata domin su bunkasa. 

Wannan ba hujjar ka’ida ba ce kawai a gare ni. Ta samo asali ne daga kwarewata wajen samar da hanyoyin fasaha a Nijeriya da kuma yin aiki tare da cibiyoyi wadanda dole ne su gudanar da ayyukansu bisa la’akari da yanayin da muke ciki. Ta hanyar wannan aiki, na ga muhimmancin tsara fasaha bisa la’akari da mutane, ababen more rayuwa, hanyoyin gudanar da aiki da kuma yanayin tattalin arzikin da aka tsara fasahar domin ta yi wa hidima. Wannan kwarewa ta kara karfafa imanin da nake da shi cewa Afirka ba za ta tsayawa kawai wajen amfani da fasaha ba; dole ne mu kara zama masu kirkirarta da mallakarta.  

“Babbar hanyar magance matsalolin Afirka ita ce hanyar da ’yan Afirka suka samar. Dole ne mu gina, mu mallaki kuma mu dore kan hanyoyin magance matsalolin da aka tsara su bisa yanayinmu; bai kamata kawai mu rika shigo da hanyoyin da aka tsara su domin yanayin wasu ba.”  

ADVERTISEMENT

Wannan ba yana nufin cewa bai kamata mu koyi darasi daga sauran sassan duniya ba ne. Akasin haka, Afirka ya kamata ta koyi darasi, ta yi hadin gwiwa, ta rungumi fasahohin da suke da amfani, sannan ta amfana da ilimin duniya. Amma koyo da wasu bai kamata ya zama abin dogaro na dindindin kan hanyoyin magance matsaloli da aka samar domin wuraren da suke da al’adu, tattalin arziki, ababen more rayuwa, cibiyoyi da kalubale daban da namu ba.  

Hanyar magance matsala da ke aiki yadda ya kamata a wani wuri, na iya kasa aiki a Afirka ba tare da an yi mata gagarumin gyara da daidaitawa da yanayinmu ba.  

LABARAI MASU NASABA

Shekaru 6 Bayan Zanga-zangar #EndSARS: Abubuwa 8 Da Suka Girgiza Nijeriya

Bankin Duniya Da IMF Sun Yi Gargaɗi Kan Barazanar AI Na Rasa Ayyukan Yi A Nijeriya

kalubalen da muke fuskanta galibi na musamman ne. Daga fannin ilimi da kiwon lafiya zuwa noma, sufuri, ayyukan kudi, fasaha, tsaro da gudanar da harkokin gwamnati, yanayin Afirka na bukatar tunanin ’yan Afirka. Muna bukatar hanyoyin magance matsaloli da suka fahimci al’ummominmu, ababen more rayuwarmu, kasuwanninmu, harsunanmu, albarkatunmu da kuma yadda al’ummarmu ke rayuwa da gudanar da ayyukansu a zahiri. 

Abu mafi muhimmanci shi ne, bai kamata mu tsaya kawai wajen amfani da hanyoyin magance matsaloli ba; dole ne mu zama masu kirkirarsu da mallakarsu.  

Lokacin da masu habaka fasaha na Afirka suka samar da fasahar Afirka, ’yan kasuwar Afirka suka kirkiri harkokin kasuwancin Afirka, masu binciken Afirka suka nemo hanyoyin magance kalubalen Afirka, sannan cibiyoyin Afirka suka zuba jari a kirkire-kirkiren Afirka, muna samar da fiye da kayayyaki kawai. Muna samar da ilimi, ayyukan yi, hakkin mallakar fasaha, kwarewa da kuma, ‘yancin dogaro da kanmu na dogon lokaci.  

Manufar bai kamata ta kasance kin duk wani abu na kasashen waje ba. Manufar ita ce mu sauya daga dogaro zuwa hadin gwiwa, daga amfani da abin da aka samar zuwa kirkirawa da kanmu, sannan daga karbar hanyoyin da wasu suka samar zuwa mallakar su. Afirka tana da matasa masu yawa kuma adadinsu na karuwa, wadanda kuma suke kara dogaro da fasaha. Wannan babbar dama ce. Bai kamata karni na gaba ya taso da imanin cewa duk wata muhimmiyar hanyar magance matsala dole ne ta fito daga wajen nahiyar ba.  

Ya kamata su ga kansu a matsayin injiniyoyi, masana kimiyya, ’yan kasuwa, masu bincike, masu zane-zane, masu kirkire-kirkire, masu tunani mai zurfi da masu iya magance matsaloli, wadanda za su iya kirkirar hanyoyin da za su amfani Afirka, daga baya kuma duniya baki daya.  

Haka kuma, ya kamata a gina hanyoyin magance matsalolin Afirka ta yadda za su dore. Samar da wani samfur ko fasaha mataki ne na farko kawai. Dole ne mu gina kwarewar da za ta ba mu damar kula da hanyoyinmu, inganta su, samar da kudaden gudanar da su da kuma fadada amfani da su.  Mallaka na nufin daukar nauyi. Yana nufin zuba jari wajen baiwar ’yan kasa, habaka cibiyoyi, kare hakkin mallakar fasaha, da kuma samar da yanayin da kirkire-kirkire za su iya rayuwa kuma su ci gaba ko da wadanda suka fara su sun daina jagorantar su.  

Kuma idan wata hanyar magance matsala da aka kirkira a Afirka ta yi nasara, bai kamata amfaninta ya tsaya a Afirka kawai ba. Hanyar da aka tsara bisa yanayin Afirka na iya zama hanyar magance matsalar duniya baki daya a karshe. Yawancin kalubalen da Afirka ke fuskanta karancin albarkatu, yawan matasa, karancin ababen more rayuwa, karancin shigar da mutane cikin harkokin kudi, matsalolin samun ilimi da kuma al’ummomin da ke warwatse ba kalubalen Afirka kadai ba ne. 

Wani lokaci, warware wata matsala mai wahala da Afirka ke fuskanta na iya haifar da daya daga cikin hanyoyin magance matsaloli mafi kirkira da ban mamaki a duniya. 

Shi ya sa dole ne mu yi imani da damar da muke da ita ta kirkira. 

Dole ne mu gina ba don sauran duniya ta gaza taimaka mana ba, sai don mun fahimci yanayinmu sosai har za mu iya kirkirar wani abu da ya fi dacewa da wannan yanayin. 

Makomar Afirka bai kamata ta kasance kawai makoma ce da ’yan Afirka za su samu damar amfani da hanyoyin magance matsaloli da duniya ta samar ba. 

Ya kamata ta kasance makoma ce da Afirka za ta kasance daya daga cikin wuraren da ake kirkirar hanyoyin magance matsalolin duniya. 

Makoma ce da ba za mu tsaya kawai wajen daidaita fasaha da yanayinmu ba, sai dai mu taka rawa wajen tsara yadda za ta kasance. Inda ba za mu kasance masu amfani da kirkire-kirkire kawai ba, sai dai mu ba da gudummawa wajen samar da su. Inda ba za mu kasance masu shiga cikin tattalin arzikin fasahar duniya kawai ba, sai dai mu gina, mu mallaki kuma mu dore da kayayyaki, ilimi, kamfanoni da hakkin mallakar fasaha da ke taka muhimmiyar rawa wajen tsara wannan tattalin arziki. 

Dole Afirka ta gina bisa yanayin da take ciki, tare da burin samar da abubuwan da za su amfani duniya baki daya. 

Nafiu Yakubu kwararren mai gina fasaha ne kuma mai kirkire-kirkire da ke aiki a fannoni daban-daban da suka hada da ilimi, basirar wucin gadi, fasahar gajimare, tsarin dijital da kuma fasahohin da ke tasowa. Ayyukansa sun fi mayar da hankali kan samar da hanyoyin fasaha masu amfani a aikace, gina kayayyakin dijital da kuma amfani da fasaha wajen magance kalubalen da ake fuskanta a zahiri.  

Afirka
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Samar Da Kayayyakin Cikin Gida Na Da Muhimmanci Wajen Ƙarfafa Tattalin Arziki – Dangote
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki

MASU ALAKA

Shekaru 6 Bayan Zanga-zangar #EndSARS: Abubuwa 8 Da Suka Girgiza Nijeriya
Rahotonni

Shekaru 6 Bayan Zanga-zangar #EndSARS: Abubuwa 8 Da Suka Girgiza Nijeriya

October 20, 2026
Bankin Duniya Da IMF Sun Yi Gargaɗi Kan Barazanar AI Na Rasa Ayyukan Yi A Nijeriya
Rahotonni

Bankin Duniya Da IMF Sun Yi Gargaɗi Kan Barazanar AI Na Rasa Ayyukan Yi A Nijeriya

October 13, 2026
Za A Ci ’Yan Siyasa Masu Kalaman Ɓatanci Tarar Miliyan 10 Da Ɗaurin Watanni 12 — INEC
Rahotonni

Jam’iyyu Da Ƴan Takara Sun Yi Wa INEC Bore Kan Cire Sunayensu Daga Takara

October 12, 2026
Next Post
Yarjejeniyar Zaman Lafiya

2027: Gwamnatin Kebbi Ta Gargaɗi Matasa Kan Bangar Siyasa

LABARAI MASU NASABA

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

October 23, 2026

Shugabar Jaridar LEADERSHIP Ta Halarci Bikin Aza Harsashin Cibiyar Ƙirƙire-Ƙirƙire Tare Da Remi Tinubu A Abuja

October 23, 2026
Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

October 23, 2026
An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

October 23, 2026
Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

October 23, 2026
Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

October 23, 2026
Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

October 23, 2026
Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina

Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina

October 23, 2026
Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’

Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.