Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya ya yi alƙawarin gudanar da bincike a kan zargin cirar kuɗaɗen garatuti na ‘yan fansho ba bisa ƙa’ida ba a gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje.
A yayin ƙaddamar da kashi na biyu na biyan kuɗin ƴan fansho na garatuti da na waɗanda suka mutu wanda ya kai har Naira biliyan ₦5b ga kusan ma’aikata 4,000 da suka yi ritaya, gwamnan ya ce sun gano rashin bayanan kuɗaɗen fansho da aka cire.
Gwamna Yusuf ya buƙaci ƙungiyar ’yan fansho ta ƙasa (NUP) reshen jihar da ta nemi a gudanar da bincike kan kuɗaɗen da suka bata. Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta fara gudanar da cikakken bincike, tare da yin alƙawarin hukunta duk wanda aka samu da hannu wajen karkatar da kuɗaɗen fansho.
Gwamnatin jihar na da burin taimakawa wajen kwato da mayar da kuɗaɗen da aka cire ga waɗanda suka yi ritaya da zarar an kammala bincike.
Gwamna Yusuf ya ƙara da cewa, kashi na farko na biyan kuɗin ya raba Naira biliyan ₦6b ga waɗanda suka ci gajiyar tallafin, inda yanzu adadin ya kai Naira biliyan ₦11b.
Ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa na tabbatar da cewa ma’aikatan da suka yi ritaya da kuma iyalan ma’aikatan da suka rasu sun samu haƙƙoƙinsu.