Majalisar Dattawan Nijeriya, ta ce murabus din alkalin alkalai, Mai Shari’a Tanko Muhammad, ba zai hana a ci gaba da yin bincike a kansa ba, kan zargin da wasu alkalan kotun koli ke masa.
A ranar Lahadi, Mai Shari’a Muhammad ya ajiye mukaminsa na alkalin alkalai, kan dalilin rashin lafiya, kuma tuni aka maye gurbinsa da mutumin na biyu mafi girman mukami a kotun koli, Mai Shari’a Olukayode Ariwoola.
- NDLEA Ta Gudanar Da Bikin Ranar Yaki Da Sha Da Fataucin Miyagun Kwayoyi Na Duniya A Kebbi
- Majalisar Dokokin Zamfara Ta Amince Da Dokar Hukunta ‘Yan Bindiga Da Sauran Laifuffuka
Alkalai 14 na kotun koli ne suka shigar da korafi kan tsohon alkalin alkalan mai murabu, suna zarginsa da yin biris da hakokinsu da kin sanyasu a harkokin kotun, wanda hakan ya sake dagula harkokin kotun da kuma tasiri a shari’o’i.
Amma Mai shari’a Muhammad ya musanta wadannan zarge-zargen tare da yin Allah-wadai.
Duk da cewa alkalin alkalan ya yi murabus, majalisa, bayan kudiri da aka gabatar gabanta a ranar Talata, ta bukaci kwamitinta ya ci gaba da binciken da kuma samar da maslaha kan dambarwar.
Majalisar ta bukaci kwamitin ya tattauna da masu ruwa da tsaki domin nazartar korafe-korafen da alkalan kotun koli suka gabatar.
Masu ruwa da tsakin za su kasance daga kowanne bangarori uku na gwamnati.
Majalisar ta kuma yi addu’a samun lafiya ga alkalin alkalan da ya yi murabus.