Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Erik ten Hag, ya bayyana cewa dole ne sai ‘yan wasan kungiyar sun sake dagewa idan har suna fatan samun irin nasarar da suke bukata a kakar wasa mai zuwa.
Manchester United ta doke Liverpool da ci 4-0 a wasan sada zumunta da suka buga ranar Talata a filin Rajamangala National a Bangkoko, kuma kungiyoyin biyu sun buga wasan ne domin gwada ‘yan wasan da za su buga musu kakar bana da za’a fara a farkon makon Agusta.
Manchester United ta fara cin kwallo a minti na 12 da fara wasa ta hannun dan wasa Jadon Sancho, sannan Fred ya kara ta biyu, minti uku tsakani kuma dan wasa Anthony Martial ya ci ta uku. Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne United ta kara ta hudu ta hannun Facundo Pellistri.
‘Yan wasa 11 da suka fara buga wasan sada zumuntar:
Liberpool ‘yan wasa 11: Alisson, Mabaya, Phillips, Gomez, Chambers, Henderson, Morton, Carbalho, Elliott, Diaz, Firmino. Man Utd ‘yan wasa 11: De Gea, Dalot, Lindelof, Barane, Shaw, McTominay, Fred, Sancho, Fernandes, Rashford, Martial. Wasannin da Liberpool za ta buga kafin fara kakar bana:
12 Yuli: Liverpool 0-4 Manchester United (Rajamangala Stadium, Bangkok) 15 Yuli: Liberpool da Crystal Palace (National Stadium, Singapore) 21 Yuli: RB Leipzig da Liberpool, (Red Bull Arena, Leipzig), 27 Yuli: Salzburg da Liverpool, (Red Bull Arena, Leipzig) 30 Yuli: Liberpool da Manchester City (Community Shield: King Power Stadium, Leicester) 31 Yuli: Liverpool da Strasbourg (Anfield) Wasannin da Manchester United za ta yi kafin fara kakar bana: 12 Yuli: Manchester United 4-0 Liberpool (Rajamangala Stadium, Bangkok) 15 Yuli: Melbourne Bictory da Manchester United (MCG, Melbourne) 19 Yuli: Manchester United da Crystal Palace (MCG, Melbourne) 23 Yuli: Manchester United da Aston Billa (Optus Stadium, Perth) 30 Yuli: Atletico Madrid da Manchester United (Ullebaal Stadion, Oslo) 31 Yuli: Manchester United da Rayo Ballecano (Old Trafford)