Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa Majalisar Zartaswa ta Ƙasa ta yanke shawarar yin amfani da rahoton yi wa ma’aikatu da hukumomin Gwamnatin Tarayya garambawul na kwamitin Steve Oronsaye ne domin a rage yawan kashe kuɗaɗen tafiyar da ayyukan gwamnati.
Idris ya ce a karkashin tsarin, wasu Ma’aikatun da Sassa da Hukumomi da Cibiyoyi za a rushe su, sannan za a haɗe wasu da wasu, wasu kuma za a maida su cikin hukumomin gwamnati da suka cancanta.
Ya ce dalilin yin hakan shi ne don gwamnati ta rage kashe kuɗaɗe, amma ba don a kori ma’aikata ba.
Ministan, wanda shi da takwaransa na kudi suka yi karin haske ga manema labarai bayan kammala majalisar zartarwa na makon nan ranar Litinin, ya ce nan gaba kadan za a ji adadin yawan ma’aikatu da hukumomin da abin ya shafa ba da daɗewa ba, yayin da aka kafa kwamitin da zai zartar da wannan aiki.
Dangane da batun masu tafiya yajin aiki, Idris ya ce gwamnati ta cika fiye da kashi 85 bisa 100 na yarjejeniyar da ta cimma da Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) a cikin 2023.
Ministan ya buƙaci shugabannin ƙungiyar ƙwadago da su dubi irin ƙoƙarin da gwamnati ke yi wajen ganin ta magance ƙalubalen da ƙasar nan ke fuskanta.
Ya ce bai kamata ‘yan ƙwadago su bayar da wata kafa wadda waɗanda ba su yi wa ƙasar nan fatan alheri ka iya kawo ruɗani a wannan mawuyacin halin da ake ciki ba.
Haka nan kuma Majalisar Zartaswa ta amince a ci gaba da biyan kuɗaɗen tallafin marasa galihu a ƙarƙashin shirin NSIP.
Ministan Kuɗi Da Kula Da Tattalin Arziki, Mista Wale Edun, cewa ya yi za a ɗauki matakan da suka dace domin tantance waɗanda suka cancanta su ci gajiyar tallafin.
Ya ce dukkan waɗanda za su ci gajiyar tallafin za a tantance su ne ta hanyar lambar sirri ta asusun bankin su (BVN) da kuma lambar shaidar ɗan ƙasa (NIN), sai kuma lambar asusun bankin su, ko da bayan an biya su kuɗaɗen ne.
Edun ya ce sake farfaɗo da shirin bayar da tallafin kuɗaɗen ya zo daidai ne lokacin da wannan gwamnati ke ƙara azamar magance ƙalubalen tsadar rayuwa da marasa galihu ke fuskanta.
Ya ce magidanta miliyan 12 ne za su ci moriyar shirin, kuma nan ba da daɗewa ba ne za a fara tura masu N25,000 daga shirin na NSIP.