Tsohon Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), Abdulrasheed Bawa, yana hannun jami’an tsaro na farin kaya (DSS) mako guda bayan dakatar da shi.
Ko da yake har yanzu jami’an ‘yansandan sirri ba su yi wani bayani ba a kan tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, an samu labarin cewa ana ci gaba da tuhumar Bawa kan rawar da ya taka wajen sake fasalin kudin kasar nan.
- Sin Ta Yi Kira Da A Goyi Bayan CAR A Yunkurinta Na Shimfida Zaman Lafiya
- RMAFC Ta Musanta Rahotonnin Karin Albashi Ga Masu Rike Da Mukaman Siyasa
Wata majiya ta ce akwai wasu batutuwan da ake tuhumarsa amma rawar da ya taka a cikin matsalar kudi a watan Fabrairun ya wuce batunsa.
Idan dai za a iya tunawa, nan take jami’an SSS suka dauke shi jim kadan bayan dakatar da shi da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi masa.
A halin da ake ciki, masu rajin kare hakkin bil’adama da kungiyoyin farar hula, sun nuna rashin amincewa da ci gaba da tsare tsohon shugaban hukumar EFCC, inda suka yi kira ga ‘yansandan sirri da su gurfanar da shi a kotu ko kuma a sake shi.
Wani mai fafutukar kare hakkin bil’adama, Salihu Aliyu, ya ce, “Ya kamata hukumar SSS ta gaggauta bincikar wadannan mutane, ina nufin Bawa da (Godwin) Emefiele, musamman (Bawa), ta gurfanar da su a kotu, ba mu ma san laifinsa ba!”
Kokarin jin martani a hukumance daga bakin kakakin hukumar DSS, Peter Afunanya, ya ci tura yayin da ya ki kiran wayarsa.
Har yanzu bai mayar da martani kan sakon da aka aike masa ba har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto.